Sarkin Musulmi ya naɗa gwamnan Zamfara sarauta

Sarkin Musulmi ya naɗa gwamnan Zamfara sarauta

- Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III ya nada gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle sarautar Shettiman Sokoto

- Sarkin Musulmin ya ce ya nada Matawalle sarautar ne don irin gudunmawa da girmama masarautun gargajiya

- A baya ma, masarautar Daura ta nada gwamna Matawalle sarautar Barden Hausa

Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya naɗa gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle "Shettiman Sakkwato".

A cikin wasikar da ke ɗauke da sanarwar zuwa ga Gwamna Matawalle, mai ɗauke da sa hannun Sarkin Musulmi, Sultan ya ce ya naɗa masa sarautar ne don mutunci da girmamama masarautun gargajiya.

Sarkin Musulmi ya naɗa Matawalle sarauta
Sarkin Musulmi ya naɗa Matawalle sarauta. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mijina ya yi min ƙaryar nice matarsa ta biyu, alhalin nice ta shida - Mata ta shaidawa kotu

"Mun gamsu da irin mutunci da girmamawa da kulawa da ka ke bawa masarautun gargajiya da ya inganta alaƙarka da fadar Sarkin Musulmi" a cewar wasikar.

Wasikar ta ƙara da cewa masarautar musulmi ta gamsu da nasarorin Mista Matawalle kan tsaro da ya kawo zaman lafiya a jihar.

Idan za a iya tunawa, masarautar Daura ita ma ta naɗa Gwamna Matawalle sarautar Barden Hausa.

KU KARANTA: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

Sarkin Daura ya ce sai da ya tuntuɓi sauran jihohin Hausawa kafin naɗin sarautar.

A wani labarin, an samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan 'yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma'aikatar JinKai da Kare Bala'i.

The Channels tv ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma'aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk ke kare kasafin kudin ma'aikatar ta.

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun damu akan yadda aka kashewa ma'aikatar kudi, da kuma rashin gabatar da wasu takardu da minista Sadiya Umar Farouk bata yi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164