Sabuwar Cutar Mashako Ta Bulla a Kano, Ana Fargabar Mutane da Dama Sun Mutu
- Rahotanni sun bayyana cewa wata sabuwar kwayar cutar mashako ta bulla a jihar Kano inda ta lakume rayukan akalla mutane 40
- Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa ana samun mace mace a kullum a asibitin IDH na Kano tun bayan bullar cutar diphtheria
- Hukumar kula da asibitocin Kano ta ce tana gudanar da taron gaggawa kan lamarin yayin da asibitin IDH ya cika makil da majinyata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Wata sabuwar cutar mashako ta lakume rayukan mutane sama da 40 wadanda yawancinsu kananan yara ne a jihar Kano.
An kwantar da gomman mutane a asibiti sakamakon kamuwa da kwayar cutar ta diphtheria.
Jaridar Daily Trust ta ziyarci asibitin IDH na Kano a ranar Laraba, inda ta rahoto cewa dukkanin sassa uku na asibiti sun cika makil da majinyata, wasu da jiran ganin likita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane na mutuwa daga cutar Diphtheria
Wani jami'in asibitin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ba da rahoton cewa kusan kullum sai an samu asarar rayuka daga wadanda suka kamu da cutar.
A cewarsa:
"A cikin makonni biyu da suka gabata, ana samun mace-mace a kullum daga wannan cutar, kullum sai likitoci sun gana da majinyata."
"Idan ka zo asibitin da safe ko da yamma, za ka tarar da gomman marasa lafiya suna jiran a duba su. tun bayan barkewar cutar muke karbar marasa lafiya."
Bullar cutar Diphtheria a Kano
Jami'in ya bayyana cewa mutane sun yi wa asibitin yawa a halin yanzu, kuma wadanda suka kamu da mashako na zuwa ne daga kananan hukumomi daban daban.
"Da yawan marasa lafiyan kanzo asibitinmu ne saboda shi ne mai dauke da kayan zamani na yaki da cututtuka, wannan ya sa yanzu asibitin a cike ya ke."
- A cewar jami'in.
Da aka tuntubi Samira Sulaiman, kakakin hukumar kula da asibitocin Kano kan lamarin, ta ce suna gudanar da taron gaggawa kan lamarin tare da yin alkawarin fitar da rahoto.
Diphtheria: An kwantar da mutum 130 a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar mashako da aka fi sani da diphtheria a turance a jihar Kano.
An ce akalla mutane 130 ne aka kwantar da su a asibiti sakamakon kamuwa da cutar yayin da gwamnatin jihar ta bude cibiyoyin yaki da cutar guda uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng