Hankula Sun Kwanta da Sojoji Suka Fadi Lokacin Dakile Matsalar tsaro, an Samu Cigaba

Hankula Sun Kwanta da Sojoji Suka Fadi Lokacin Dakile Matsalar tsaro, an Samu Cigaba

  • Yayin da ake fama da matsalar tsaro a Najeriya, hafsan sojojin kasar ya kwantarwa al'umma hankulansu game da haka
  • Hafsun dakarun sojojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ba da tabbacin dakile matsalolin tsaron nan ba da jimawa ba
  • Hakan ya biyo bayan yawan samun cikas musamman a yankunan Arewacin Najeriya da ake fama da ta'addanci da satar mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja ya ba da tabbaci kan kawo karshen rashin tsaro.

Hafsan sojojin ya ce rashin tsaron Najeriya ya kusa zuwa karshe duba da rahotanni da suke samu daga kwamandojinsu.

Sojoji sun sha alwashin dakile matsalolin tsaron Nijeriya baki daya
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja ya ba da tabbacin kawo karshen matsalar tsaro. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Sojoji sun shirya dakile matsalar rashin tsaro

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan bindiga akalla 8 sun baƙunci lahira da suka yi arangama da sojoji

Janar T. Lagbaja ya bayyana haka ne a yau Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 yayin taron tsaro a Akwa Ibom, Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lagbaja ya ce sojoji na samun galaba duba da rahotanni da suke samu daga kwamandojinsu a yankuna daban-daban, cewar Vanguard.

Hafsan sojoji ya fadi cigaba da aka samu

"Dole mu fada muku muna cin galaba kan yan ta'adda, rahotanni da muke samu daga kwamandojinmu sun tabbatar da cewa muna kan hanya mai kyau."
"Rashin tsaron da ke damun Najeriya mai wucewa ne kuma za mu kawo karshensa nan ba da jimawa ba."
"Ina mai tabbatar muku da cewa rundunar sojoji ta himmatu wurin dakile matsalar tsaro tare da hadin kan sauran hukumomin tsaro."

- Taoreed Lagbaja

Lagbaja ya ce an shirya taron ne domin tabbatar da nasarorin da suke samu yayin daukar wasu matakai a kokarin dakile matsalolin tsaron kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: CBN ya fadawa 'yan Najeriya gaskiyar halin da za a shiga

Hafsan sojoji ya kai ziyara Nijar

A wani labarin, kun ji cewa Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gana da takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Janar Mousa Barmo.

Wannan ziyara na zuwa ne bayan gwamnatin Sojin Nijar ta fice daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS).

Masani kuma mai sharhi da bibiyar harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya tabbatar da hakan a shafinsa na manhajar X.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.