Za a Samu Sauki: Gwamnati Ta ba 'Yan Kasuwa Wa’adin Karya Farashin Kayayyyaki

Za a Samu Sauki: Gwamnati Ta ba 'Yan Kasuwa Wa’adin Karya Farashin Kayayyyaki

  • Gwamnatin tarayya ta ba 'yan kasuwa da masu ruwa da tsaki wa'adin kwanaki 30 su sauke farashin kayayyaki kafin ta fara daukar mataki
  • Gwamnatin ta ce lallai za ta tilasta sauke farashin kayan masarufi a kasar da zarar wa'adin wata daya da ta ba 'yan kasuwar ya kare
  • Legit Hausa ta leka kasuwar Bacci da ke jihar Kaduna inda ta ji farashin wasu daga cikin kayan abinci da aka fi amfani da su a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar FCCPC ta ba ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki da ke da hannu a tsadar kayayyaki wa’adin wata daya su sauke farashin kayayyakin.

Kara karanta wannan

Zamfara: Gwamna ya ba da tallafin kudi da filaye ga wadanda ambaliya ta shafa

Mataimakin shugaban hukumar FCCPC, Mista Tunji Bello, ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan tsawwala farashin kayayyaki a ranar Alhamis a Abuja.

Gwamnati ta yi magana kan rage farashin kayayyakin masarufi a kasar
Gwamnatin tarayya ta ba 'yan kasuwa wa'adin sauke farashin kayan masarufi. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An ba 'yan kasuwa wa'adin karya farashi

A cewar Mista Bello, hukumar za ta fara aiki tabbatar da wannan doka bayan cikar wa'adin, inji rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce taron an yi shi ne domin magance karuwar hauhawar farashin kayan masarufi da kuma munanan dabi'un da wasu 'yan kasuwa ke nunawa.

Sabon mataimakin shugaban FCCPC ya ba da misali da cewa:

"Akwai wani dan itace da aka fi sani da Ninja da ake sayar da shi kan $89 (N140,000) a Texas, mun gano ana sayar da shi kan N944,999 a Victoria Island, jihar Legas."

Hukuncin tsawwala farashin kaya

Mista Bello ya nuna mamakinsa kan dalilin tashin gwauron zabin dan itacen a nan Najeriya idan aka kwatanta da Texas ta Amurka, bambancin da ya ce ya wuce kima.

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

The Punch ta ruwaito mataimakin shugaban hukumar ya ce tsawwala farashin kayayyaki da kuma kayyade farashin na yin barazana ga zaman lafiyar tattalin arzikin kasar.

“A karkashin sashe na 155, masu wannan dabi'a walau daidaikun mutane ko kamfanoni za su fuskanci hukunci mai tsanani da ya hada da tara da dauri idan aka same su da laifi."

- Tunji Bello.

Ya farashin kayan ya ke yanzu?

A zantawarmu da Muhammadi Cigari, wani dan kasuwa a kasuwar Bacci, jihar Kaduna, ya ce har yanzu dai farashin wasu kayayyakin abinci bai sauko ba, amma na wasu ya sauko.

Ya ce a yanzu buhun shinkafa ya N84,000 zuwa N85,000 yayin da taliya ta ke a N20,000. Buhun sukari kuwa ana samunsa a N82,000.

Malam Cigabari ya ce fulawa kuwa ta kai N65,000 a yanzu. Sai dai dan kasuwar ya ce farashin ba tsayawa ya ke yi, yana hawa yana sauka, sannan ya danganta ne da kamfanin da mutum zai saya.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa gwamnatin Sokoto ba ta biya kudin fansar Sarkin Gobir ba

Farashin kayan masarufi ya tashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa frashin kayayyaki a Najeriya ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai kashi 34.19% a watan Yunin 2024.

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta rahoto cewa farashin ya tashi ne daga kashi 33.95% a watan Mayu bayan da ta yi amfani da sauyin farashin kayayyaki na CPI.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.