Shugaba Bola Tinubu Ya Lula Zuwa Ƙasar China, Zai Tsaya a Wata Ƙasa a kan Hanya
- Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya bar babban birnin tarayya Abuja zuwa ƙasar China inda zai kai ziyarar aiki
- Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Tinubu zai tsaya a UAE
- Wannan ziayara na zuwa ne a daidai lokacin da wani kamfanin China ya ƙwace jiragen shugaban kasa a ƙasar Faransa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bar babban birnin tarayya Abuja zuwa ƙasar Sin watau China, inda zai kai ziyarar aiki.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya ce Bola Tinubu zai ɗan tsaya a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) kafin daga bisani ya wuce China.
Cif Ngelale ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayyukan da Bola Tinubu zai yi a China
"Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai tashi daga Abuja ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024 zuwa birnin Beijing na kasar Sin domin ziyarar aiki.
"Shugaban zai tsaya wata ƴar taƙaitacciyar ziyara a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE). Yayin ziyarar aiki a Sin, Tinubu zai gana da Shugaba Xi Jinping da kuma ƴan kasuwa.
"A gefe guda kuma shugaban kasarzai halarci taron tattaunawa kan alaƙar China da nahiyar Afirka," in ji sanarwar.
Kamfanin China ya ƙwace jiragen Najeriya
Wannan ziyara ta Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da wani kamfani mai suna Zhongshan Fucheng daga China ya kwace jiragen Najeriya.
Kwanan nan wata kotu a Faransa ta yanke hukunci kan taƙaddamar, inda ta ba kamfanin izinin kama jiragen shugaban kasa mallakar gwamnatin Najeriya.
Mai girma Shugaba Tinubu ya tafi wannan ziyarar aiki tare da rakiyar manyan ƙusoshin gwamnatin Najeriya.
Da zarar an gama taron da za a yi, zai kamo hanyar dawowa birnin tarayya Abuja.
Tinubu ya dawo da tallafin lantarki
Kuna da labarin gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta maido tallafin wutar lantarki da kashi 50% ga dukkan asibitocin gwamnati a fadin ƙasar nan.
Ministan lafiya da walwalar al'umma, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng