'Yan Ta'adda Masu Yawa Sun Sheka Barzahu bayan Sojoji Sun Yi Musu Ruwan Wuta

'Yan Ta'adda Masu Yawa Sun Sheka Barzahu bayan Sojoji Sun Yi Musu Ruwan Wuta

  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta samu nasara kan ƴan ta'addan da ke addabar bayin Allah a yankin Arewa maso Gabas
  • Jiragen rundunar sun yi ruwan wuta kan maɓoyar ƴan ta'addan da ke a yankin Tumbun kusa da tafkin Chadi
  • Sakamakon ruwan wutan da jiragen dakarun sojojin suka yi, an hallaka ƴan ta'adda masu yawa tare da lalata kayayyakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kai hare-hare kan ƴan ta'aɗɗa a jihar Borno.

Rundunar sojojin saman ta ce hare-haren da aka kai a yankin Tumbun da ke kusa da tafkin Chadi, sun yi sanadiyyyar hallaka ƴan ta'adda masu yawa.

Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'adda a Borno
Sojojin sama sun sheke 'yan ta'adda a Borno Hoto: SODIQ ADELAKUN/AFP
Asali: Getty Images

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Manjo Janar Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan bindiga akalla 8 sun baƙunci lahira da suka yi arangama da sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun yi nasara kan ƴan ta'adɗa

Kakakin ya bayyana cewa an samu nasarar kai hare-haren ne bayan ruwan sama ya tilastawa ƴan ta'addan komawa kan tsaunuka sakamakon cika da ruwa da maɓoyarsu ta yi, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Manjo Janar Edward Gabkwet ya tabbatar da cewa dakarun rundunar sun yi leƙen asiri kan wuraren a ranakun 22, 24 da 26 na watan Agustan 2024.

Ya ƙara da cewa sun gano ƴan ta'adda masu yawa a cikin wasu tantuna guda uku da aka yi su a ƙasan bishiyoyi.

Sojojin sama sun sheƙe ƴan ta'adda

"A wani babban koma baya ga ragowar ƴan ta'addan da ke ɓoye a yankin Tumbun kusa da Tafkin Chadi, sojojin sama na Operation Hadin Kai sun kai hare-hare a Jubillaram, da ke Kudancin Tumbun."

- Manjo Janar Edward Gabkwet

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna, sun cafke mai ba su bayanai

Ya bayyana cewa hare-haren sun yi sanadiyyar hallaka ƴan ta'addan tare da lalata kayayyakinsu.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa jiragenta sun kai farmaki kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihohin Kaduna da Zamfara.

Rundunar sojojin saman ta bayyana cewa a yayin farmakin, dakarunta sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa a jihohin guda biyu na yankin Arewa masi Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng