'Yan Bindiga Sun Yi Kwanton Bauna a Kauye, Sun Budewa Shugaban Tsaro Wuta

'Yan Bindiga Sun Yi Kwanton Bauna a Kauye, Sun Budewa Shugaban Tsaro Wuta

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Anambra na nuni da cewa yan bindiga sun mamaye wani kauye kuma suka harbi shugaban tsaron garin
  • Mummunan lamarin ya faru ne a yankin Obosi a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra kamar yadda bayanai suka tabbatar
  • Bayan sun harbi mutumin, shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa yan bindigar sun harbi motarsa kafin su cinna mata wuta daga baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - Wasu miyagu yan bindiga sun kai farmaki wani kauye a jihar Anambra inda suka kai farmaki kan shugaban tsaro.

An ruwaito cewa yan bindigar sun biyo shugaban tsaron garin ne yayin da yake tafiya a cikin motarsa zuwa gida.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi awon gaba da babban jami'in gwammati a Najeriya

Yan sanda
Yan bindiga sun kai hari Anambra. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban tsaron mai suna Dan Igbokwubili ya kasance tsohon dan sanda ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun mamaye gari

Rahotanni da suka fito daga Anambra sun nuna cewa yan bindiga sun biyo wani shugaban tsaro yana tafiya gida a yankin Oboso.

Lamarin ya faru ne da dare inda suka yi kwanton ɓauna suka fara harbi kan motar Dan Igbokwubili a lokacin da suka hango shi yana tahowa.

Sarkin garin, Igwe Chidubem Iweka ya ce lamarin ya zo musu da mamaki kasancewar ba su dade da fatattakar matsafa da masu garkuwa a garin ba.

Yadda shugaban tsaro ya tsira a Anambra

A lokacin da suka fara harbin, Dan Igbokwubili ya yi maza maza ya fice daga motarsa ya kwanta yana tafiya a kasa.

A matsayinsa na tsohon dan sanda, ya kwanta a kasa kafin ya samu dama ya doki daya daga cikin yan bindigar a mazakuta sannan ya tsere zuwa asibiti.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun nuna bajintarsu, an gano yadda aka kashe fitinannen dan ta'adda

Sai dai duk da ya samu ya tsallake rijiya ta baya, yan bindigar sun harbi motarsa sosai kafin su cinna mata wuta ta ƙone.

'Yan bindiga sun kashe dan sarki a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Legas ta fitar da bayani kan yadda yan bindiga suka kashe babban dan wani mai sarauta.

Yan bindigar sun kashe dan farin sarkin mai suna Tijjani Akinloye da tsakar rana kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng