Gwamnan Yobe Ya Bayyana Matsayarsa Kan Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi

Gwamnan Yobe Ya Bayyana Matsayarsa Kan Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi

  • Gwamnatin jihar Yobe ta yi magana kan maganganun da ke nuna cewa da amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
  • Gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta musanta cewa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashin na ma'aikata a jihar
  • Ta bayyana cewa har yanzu tana ci gaba da tattaunawa kan lamarin kuma za ta sanar da halin da ake ciki da zarar an kammala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa ba ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba.

Gwamnatin ta musanta jita-jitar da ke yawo a yanar gizo kan cewa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi, inda ta bayyana hakan a matsayin ƙarya da yaudara.

Kara karanta wannan

Ana rade radin barinsa APC, gwamna ya yi sababbin nade nade a gwamnatinsa

Gwamna Yobe ya musanta amincewa da sabon mafi karancin albashi
Gwamnanatin Yobe ta musanta amincewa da sabon mafi karancin albashi Hoto: Hon Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Alhaji Mamman Mohammed, daraktan yaɗa labarai na Gwamna Mai Mala Buni ya fitar a ranar Alhamis a Damaturu, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe gwamnati za ta amince da N70,000

Alhaji Mamman ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin na ma’aikata ba.

Ya ƙara da cewa har yanzu gwamnati na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kuma za ta fitar da sanarwa a hukumance da zarar an cimma matsaya.

"Hankalin gwamnatin jihar Yobe ya kai kan wani labarin ƙarya da yaudara da aka wallafa a shafukan sada zumunta na cewa an amince da sabon mafi ƙarancin albashi."
"Gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa kan hakan ba, kuma za ta bayar da ƙarin bayani da zarar an kammala komai."

Kara karanta wannan

Sama da mutane miliyan 30 na cikin yunwa, gwamnati ta kawo hanyar wadatar da abinci

- Alhaji Mamman Mohammed

Alhaji Mamman ya kuma buƙaci jama'a da su yi watsi da labaran na ƙarya, rahoton Daily Post ya tabbatar da labarin.

Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi

Gwamnan Adamawa ya fara biyan N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Ahmadu Fintiri ya ɗauka a makon jiya cewa zai fara biyan ma'aikata sabon albashin a ƙarshen watan Agusta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng