Bikin Ranar Haihuwa: Kashim Shettima Ya Fadi Abin da Yake So daga ’Yan Najeriya

Bikin Ranar Haihuwa: Kashim Shettima Ya Fadi Abin da Yake So daga ’Yan Najeriya

  • Yayin da ake daf da gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, Kashim Shettima ya shawarci al'umma
  • Mataimakin shugaban kasar ya ce bai kamata abokan arziki da 'yan uwa su kashe kudi domin taya shi murnar ranar ba
  • Shettima ya bukace su da su yi amfani da kudin wurin taimakon marasa ƙarfi da kai kudin gidajen marayu da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ta roki yan Najeriya kan murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Sanata Kashim Shettima ya bukaci al'umma da su guji kashe kudi domin taya shi murnar cika shekaru 58 a duniya.

Kashim Shettima ya roki yan Najeriya kan bikin ranar haihuwarsa
Kashin Shettima ya shawarci al'umma kan taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Hoto: @KashimSM.
Asali: Twitter

Kashim Shettima ya roki yan Najeriya alfarma

Kara karanta wannan

Kasuwancin Arewa zai habaka, tashar tsandaurin Kebbi ta bude ofishi a Kano

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Stanley Nkwocha ya fitar a yau Alhamis 29 ga watan Agustan 2024, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban kasar ya bukaci masu son taya shi murnar su yi amfani da kudin wurin taimakon gidajen marayu.

Babu biki yayin da Shettima ya cika 58

Kashim zai cika shekaru 58 ne a ranar Litinin 2 ga watan Agustan 2024, kamar yadda TheCable ta tattaro.

Ya ce bai son gudanar da wani biki na musamman saboda murnar zagayowar ranar haihuwar tasa.

Kashim Shettima ya yi koyi da tsarin Tinubu

"Mataimakin shugaba kasa, Shettima ya shawarci yan uwa da abokan arziki da ke shirin biyan kudin talla domin ta ya shi murna su yi amfani da kudin a gidajen marayu da taimakon marasa ƙarfi."
"Wannan na daga cikin tsare-tsaren shugaba Bola Tinubu domin inganta tattalin arziki da rayuwar al'umma."

Kara karanta wannan

Kwara: Ana cikin halin kunci, dattijuwa mai shekara 54 ta haifi jarirai 11, miji ya kidime

"Shettima ya godewa al'umma kan irin goyon baya da fatan alheri da suke yi masa cikin shekaru da dama."

- Kashim Shettima

Shettima ya koka kan matsalar tsaro

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya tarayya ta bayyana cewa akwai bukatar jami'an tsaro su mayar da hankali wajen kokarin sanya ido kan al'amuran tsaro.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayar da umarnin a taron kammala karatun kwalejin tsaro ta Nigeria Defence Academy da ke Abuja.

Ya ce gwamnati na kokarin samar da yanayi mai kyau wanda zai jawo masu zuba hannun jari kasar domin bunkasa tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.