An Fafata Tsakanin Yan Sanda da Miyagu, An Kashe Fitinannen Dan Ta'adda

An Fafata Tsakanin Yan Sanda da Miyagu, An Kashe Fitinannen Dan Ta'adda

  • Rundunar yan sandan kasar nan ta yi nasarar fatattakar yan ta'adda da su ka addabi mazauna jihar Akwa Ibom
  • Yan sandan sun kashe wani shugaban masu garkuwa da mutane kuma barayin kan ruwa da su ka takurawa jama'a
  • Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar yan sandan jihar, Timfon John ce ta shaidawa manema labarai lamarin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Akwa Ibom - Yan sanda a Akwa Ibom sun yi nasarar kashe daya daga jagororin masu garkuwa da mutane a jihar bayan an fafata.

Jami'ar hulda da jama'a na rundunar, ASP Timfon John ce ta bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

Akwa Ibom
Yan sanda sun kashe fitinannen dan ta'adda a Akwa Ibom Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa jami'ar ta ce yan sanda sun bi shugaban kungiyar yan ta'adda ta bling bling har maboyarsa da ke yankin Uyanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Condiment, kasungurmin dan fashin teku ne da ya hana jama'ar yankin sakat, musamman masu hawa kan ruwa.

An kashe dan ta'adda, Condiment

Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta bayyana harbe kasungurmin mai garkuwa da mutane, 'Condiment.' Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, ASP Timfon John da ta tabbatar da hakan ta ce an yi musayar wuta kafin harbe hatsabibin, PM News ta wallafa.

An kwato makamai a hannun 'yan ta'adda

Yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kwato wasu makamai bayan sun ragargaji miyagu da su ka hana jama'a sakat a jihar.

Daga cikin makaman akwai bindiga kirar G3 rifles guda daya, sai alburusai guda hudu, kuma tuni aka aika da gawar wanda aka kashe dakin adana gawarwaki a jihar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun cika umarnin Sufeto Janar, an yi holin 'yan Shi'a a Abuja

An hallaka 'yan ta'adda 8 a Kaduna

A wani labarin, rundunar sojojin kasar nan ta kara samun nasara a kan yan ta'adda bayan jami'anta sun kashe miyagu takwas a jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna da ta tabbatar da lamarin ta ce jami'an sojojin da suka fito sintiri a karamar hukumar Birnin Gwari ne su ka aika da miyagun lahira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.