Tinubu Ya Maido Tallafin Lantarki da Kashi 50%, an Ambaci Waɗanda za Su Amfana

Tinubu Ya Maido Tallafin Lantarki da Kashi 50%, an Ambaci Waɗanda za Su Amfana

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta maido tallafin wutar lantarki da kashi 50% ga dukkan asibitocin gwamnati a fadin ƙasar nan
  • Ministan lafiya da walwalar al'umma, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar Kaduna
  • Legit ta tattauna da wata ma'aikaciyar lafiya a jihar Yobe, Amina Bulama domin jin yadda tallafin lantarki zai taimaka musu wajen aiki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - A kokarin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na saukaka rayuwa a Najeriya, ta rage kudin lantarki.

Sai dai ministan lafiya da walwalar al'umma, Dakta Tunji Alausa ya ce tallafin da aka saka ba na gama gari ba ne.

Kara karanta wannan

Likitoci sun fadi abin da ke korarsu zuwa neman aiki a kasashen waje

Bola Tinubu
Gwamnati ta saka tallafin lantarki ga asibitoci. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ministan ya fadi haka ne yayin wata ziyara da ya kai jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An maido tallafin lantarki kashi 50%

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta saka tallafin kudin lantarki ga asibitocin gwamnati a fadin Najeriya da kashi 50%.

Hakan na nuni da cewa asibitoci za su rika biyan rabin kudin wutar da suke sha sakamakon samun tallafin.

Dalilin maido tallafin lantarki a asibitoci

Ministan lafiya da walwalar al'umma, Dakta Tunji Alausa ya ce an saka tallafin ne domin rage kudin da ake kashewa a asibitoci.

Dakta Tunji Alausa ya kara da cewa rage kudin da marasa lafiya ke kashewa yayin jinya na cikin dalilan maido tallafin.

Aikin da ministan lafiya ya yi a Kaduna

Punch ta wallafa cewa Ministan lafiya ya kaddamar da na'urar tattara bayanai ta yanar gizo a asibitin tarayya da ke Barnawa a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sama da mutane miliyan 30 na cikin yunwa, gwamnati ta kawo hanyar wadatar da abinci

Haka zalika yayin ziyarar, Dakta Tunji Alausa ya kaddamar da rijiyar birtsatsi a wajen samar da wuta mai amfani da hasken rana a asibitin.

Legit ta tattauna da Amina Bulama

Wata ma'aikaciyar lafiya a jihar Yobe, Amina Bulama ta bayyana cewa tallafin lantarki zai taimakawa asibitoci da marasa lafiya.

Amina ta ce asibiti zai rage kashe kudin lantarki wanda hakan zai sa a yi amfani da kudin domin wasu ayyukan cigaba.

Cire tallafin mai ya jefa talaka a matsala

A wani rahoton, kun ji cewa kididdiga ta nuna cewa miliyoyin yan Najeriya na fama da rashin abinci wanda hakan ya taba mata da yara kanana.

An jingina dalilin fadawa cikin halin ga cire tallafin man fetur da kuma rashin tsaro da ake fama da shi musamman a jihohin Arewa ta yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng