Rai Bakon Duniya: Kwamishinan 'Yan Sanda a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Rai Bakon Duniya: Kwamishinan 'Yan Sanda a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An shiga jimami bayan rasuwar kwamishinan yan sanda a jihar Akwa Ibom, Waheed Ayilara da sanyin safiya
  • Iyalan marigayin ne suka tabbatar da haka a cikin wata sanarwa ta musamman yau Alhamis 29 ga watan Agustan 2024
  • Marigayin ya rasu ne bayan yi masa tiyatar ciwon daji a asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos da safiyar yau Alhamis

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - An shiga alhini bayan sanar da rasuwar Kwamishinan yan sanda a jihar Akwa Ibom.

Marigayi Waheed Ayilara ya rasu da safiyar yau Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 a asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali, soja ya harbe wani shugaban 'yan sanda har lahira

Kwamishinan yan sanda a Najeriya ya rasu a Lagos
Kwamishinan yan sanda a jihar Akwa Ibom, Waheed Ayilara ya bar duniya. Hoto: @officerTimzy.
Asali: Twitter

Yaushe kwamishinan yan sanda ya rasu?

The Nation ta tattaro cewa Ayilara ya rasu ne bayan yi masa tiyata a daren jiya Laraba 28 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan marigayin sun tabbatar mutuwar Ayilara a cikin wata sanarwa da suka fitar ga yan jaridu.

"Muna bakin cikin sanar da ku cewa dan uwanmu kuma aboki, kwamishinan yan sanda a jihar Akwa Ibom, Waheed Ayilara ya rasu."

- Cewar sanarwar

Mukamin da ya rike a gidan 'yan sanda

Wani babban dan sanda da ya bukaci boye sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana ba ya tabbatar da mutuwar Ayilara a yau Alhamis, kamar yadda Punch ta tattaro.

Kafin rasuwarsa, Ayilara ya rike muƙamin mukaddashin kwamishinan yan sanda a jihar Lagos wanda aka naɗa shi a watan Nuwambar 2023.

Daga bisani babban sifetan yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya naɗa shi kwamishinan yan sanda a Akwa Ibom a watan Fabrairun 2024 domin cigaba da kula rundunar jihar.

Kara karanta wannan

An shiga alhini bayan sanar da rasuwar fitaccen jarumin fina-finai a Najeriya

Tsohon kwamishinan yan sanda ya rasu

Kun ji cewa, Babban Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun ya nuna alhininsa bayan mutuwar Fatai Adio Shittu mai ritaya.

Egbetokun ya bayyana kaduwarsa ne ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba na tsohon kwamishina 'yan sandan a Najeriya.

Rahotanni sun tattaro cewa Shittu ya rasu ne a jiya Juma'a 17 ga watan Nuwambar 2024 ya na da shekaru 73 a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.