‘Bello Turji Ya Zama Hafsun Sojoji?’ Dalung Ya yi Zazzafan Martani ga Gwamnatin Tinubu

‘Bello Turji Ya Zama Hafsun Sojoji?’ Dalung Ya yi Zazzafan Martani ga Gwamnatin Tinubu

  • Tsohon ministan wasanni a Najeriya, Solomon Dalung ya yi zazzafan martani ga gwamnatin tarayya a ranar Laraba
  • Barista Dalung ya bayyana cewa a halin yanzu ba a san ko Bello Turji ne shugaban soji ko Janar Christopher Musa ba
  • Haka zalika 'dan siyasar ya yi magana kan abubuwan da suka biyo bayan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Tsohon ministan harkokin wasanni a Najeriya, Barista Solomon Dalung ya yi maganganu kan taɓarɓarewar tsaro a Najeriya.

Solomon Dalung ya kuma yi magana kan kisan sarkin Gobir da wasu abubuwa da suka biyo bayan zanga zanga tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: CBN ya fadawa 'yan Najeriya gaskiyar halin da za a shiga

Solomon Dalung
Solomon Dalung ya yi magana kan tsaro. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Barrister Solomon Dalung
Asali: Facebook

RFI Hausa ne ta sanya hirar Barista Solomon Dalung a wani bidiyo da ta wallafa a shafin Facebook a yammacin ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Solomon Dalung kan Bello Turji

Barista Solomon Dalung ya ce ya kamata jami'an tsaro da suka fito a lokacin zanga zanga su nufi jeji domin tunkarar yan ta'adda.

Tsohon ministan ya ce a yanzu haka sun gaza fahimta ko Bello Turji ne babban hafsun sojojin Najeriya duba da yadda yake cin karensa ba babbaka.

Ya ce a halin yanzu sun rikice har suna ganin cewa kamar Bello Turji ne hafsun sojojin Najeriya yadda zai fito ya yi magana da kayan sojoji kuma an gaza kama shi.

Maganar Dalung kan zanga zanga

Solomon Dalung ya ce kafin zanga zanga an koka kan abin da zai biyo baya wajen kiran mutane su hakura da fita zanga zangar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ɗauki mataki na gaba bayan ganawa a Abuja

Sai dai a cewarsa ana samun barna ko ba ta dalilin zanga zanga ba kamar yadda yan bindiga suka kashe sarkin Gobir kuma suka hana gawarsa.

Ya kara da cewa yan bindiga sun cigaba da kashe kashe da sace sace ciki har da garkuwa da mutane kimanin 150 a Sokoto.

Sojoji sun hallaka yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri a ƙauyen Kurmin Kare da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Sojojin sun hallaka wasu ƴan bindiga biyu bayan sun ritsa su a cikin daji sakamakon samun bayanan sirri da suka yi a kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng