Jigo a APC Ya Hango Illar Hana Dalibai Rubuta WAEC da NECO, Ya Ba Tinubu Shawara

Jigo a APC Ya Hango Illar Hana Dalibai Rubuta WAEC da NECO, Ya Ba Tinubu Shawara

  • Jigo a jam'iyyar APC ya fito ya yi magana kan shirin gwamnati na hana ɗalibai ƴan ƙasa da shekara 18 zana WAEC da NECO
  • Abayomi Nurain Mumuni ya bayyana cewa idan aka aiwatar da shirin akwai tarin matsalolin da zai jefa ƙasar ta bangaren ilmi
  • Abayomi ya buƙaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman daga aiwatar da shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Abayomi Nurain Mumuni, ya buƙaci Bola Tinubu ya sanya baki kan shirin hana ɗalibai ƴan ƙasa da shekara 18 rubuta jarabawar WAEC da NECO.

Jigon na APC ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman daga aiwatar da wannan sabon tsarin.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Shugaban NLC ya bar wurin ƴan sanda, ya koma hedkwatar ƴan kwadago

Jigon APC ya soki shirin gwamnati
Jigon APC ya caccaki shirin hana dalibai 'yan kasa da 18 yin WAEC da NECO Hoto: @ProfTahirMamman
Asali: Twitter

Abayomi ya buƙaci hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Rasheed Abubakar ya ba jaridar Vanguard a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Illar ƙayyade shekarun gama sakandire

Jigon na APC ya bayyana cewa matakin hana ɗaliban ƴan ƙasa da shekara 18 zana jarrabawar WAEC da NECO zai zo da illoli masu yawa.

Ya yi nuni da cewa irin wannan shirin idan aka aiwatar da shi, zai yi mummunan tasiri ga ɗalibai da al'umma gaba ɗaya.

Jigon na APC ya ƙara da cewa idan aka bari aka aiwatar da shirin, zai rage samun damar guraben yin karatu da ƙara yawan mutanen da za su riƙa barin makaranta.

Ya yi nuni da cewa idan hakan ta faru za a ƙara yawan matsaloli a cikin al'umma.

Ya yi bayanin cewa irin wannan shirin idan aka aiwatar da shi, zai jawo matasa su daɗe ba su cimma burikansu na karatu ba wanda hakan zai sanya su cikin damuwa.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Tinubu ya yi alhinin asarar da aka yi, ya dauki alkawari

Atiku ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki matakin gwamnatin Bola Tinubu na kayyade shekarun kammala sakandare.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan na Najeriya, ya ce matakin zai mayar da ƙasar nan baya, inda ya zargi gwamnati da cewa ba ta san abin da ta ke yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng