Kasuwancin Arewa zai Habaka, Tashar Tsandaurin Kebbi Ta Bude Ofishi a Kano
- Tashar tsandaurin Tsamiya da ke jihar Kebbi ta bude ofishi a Kano domin duba kayan da za a rika safararsu
- A jawabinsa yayin bude ofishin, shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi ya ce wannan muhimmin mataki ne
- Kwastam na ganin bude tsandaurin Segbana-Tsamiya zai taimaka sosai, bayan jagororin Benin da Najeriya sun gana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - A yunkurin bunkasa safarar kaya a tsakanin jihohin da ba su da teku, tsandaurin Tsamiya da ke jihar Kebbi ya bude ofishi a Kano.
Ofishin zai rika tantance kayan da za a yi safararsu zuwa sassan Arewacin kasar nan har zuwa Jamhuriyyar Benin.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa da ya ke jawabi yayin bude ofishin, shugaban hukumar kwastam na kasa, Bashir Adeniyi ya yaba da farfado da tashar tsandaurin Segbana-Tsamiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban, wanda ya samu wakilcin jami'i mai kula da yankin Zone B, Sambo Dangaladima ya ce bude farfado da tashar da bude ofishi a Kano zai habaka kasuwanci.
Najeriya-Benin: Muhimmancin tashar tsandauri
Jaridar The Nation ta wallafa cewa tun a watan Mayu, 2024 hukumomin kasar nan su ka gana da mahukunta a jamuriyyar Benin kan bude tashar tsandaurin Tsamiya.
Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi ya ce yi tattaunawar domin gano hanyoyin cigaba wajen safarar kaya tsakanin iyakokin kasashen biyu, da batun tsaro da cigaban tattalin arziki.
Yadda ofishin tashar tsandauri za ta taimaka
Mista Bashir Adeniyi ya bayyana cewa bude ofishin tashar tsandauri a Kano ya nuna muhimmancin da jihar ke da shi a matsayin cibiyar kasuwanci.
Ya ce hakan ya yi daidai da kudurin gwamnati na samar da abinci da kara kulla kawance tsakaninta da makotan kasashe.
An kaddamar da tashar tsandauri
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya za ta kaddamar da tashar tsandauri a Funtua da ke jihar Katsina domin bunkasa safarar kaya tsakanin jihohin da ba sa kusa da teku.
Tashar za ta zama ta uku, bayan wacce aka kaddamar a jihar Kaduna a shekarar 2018 da ta Dala a Kano da aka samar a shekarar 2023 duk a yunkurin saukaka shigo da kaya yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng