Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Jigilar Kaya a Jirgin Kasan Tashar Tsandauri da ke Kano

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Jigilar Kaya a Jirgin Kasan Tashar Tsandauri da ke Kano

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da jirgin kasa na farko na kaya daga tashar tsandaurin Kano zuwa tashar ruwa ta APM a Apapa da ke jihar Legas
  • Ministan Sufuri, Sa'id Ahmed Alkali da ya kaddamar da jirgin farkon ya bayyana cewa yanzu shigowa da fitar da kaya daga Arewa zai yi sauki matuka
  • Ya ce a gwajin da su ka yi, an yi nasarar sufurin kwantena 40 na kaya daga tashar tsandauri ta Dala zuwa Legas, kuma hakan zai kara bunkasa kasuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da jirgin farko na kaya daga tashar tsandauri ta Dala Inland da ke Kano zuwa tashar APM ta Apapa a Legas.

Kara karanta wannan

Alhazan Kano sun samu gata, an fara ciyar da su abinci kyauta a Saudiyya

Da yake kaddamar da tashar, ministan sufuri Sanata Said Ahmad Alkali, shigowa da fitar da kayayyaki zuwa Arewa zai yi sauki sosai.

Sen. Sa’idu Ahmed Alkali
An fara jigilar kaya daga tashar tsandaurin Kano zuwa tashar ruwa ta Legas Hoto: Sen. Sa’idu Ahmed Alkali
Asali: Facebook

A shafinsa na facebook, ministan ya bayyana yakinin samun bunkasar kasuwanci ga mazauna yankin tashar tsandaurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi nasarar safarar kwantena 40

Ministan sufuri, Sanata Sa'id Ahmad Alkali ya bayyana cewa an yi gagarumar nasara wajen fara jigilar kaya daga jirgin kasan tashar tsandauri ta Kano zuwa Legas.

Ministan ya ce an yi nasarar sufurin kwantena 40 na kaya daga Kano zuwa tashar Apapa da ke Legas a cikin 'yan kwanaki kadan.

Ya ce gwamnati ta na iya kokarinta wajen zamanantar da ayyukan sufuri, shi ne ma ya sa ta dauki gabarar gyara layin dogo na Kaduna-Kano, da ginin layin dogo daga zuwa Maradi.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

An kusa kammala layin dogon Kano-Legas

A baya mun kawo mu ku labarin cewa Ministan Sufuri, Sa'id Ahmad Alkali ya bayyana cewa layin dogon da gwamnati ta gina daga Kano zuwa Legas zai fara jigila a wayan Yuni.

A yadda gwamnati ta dauko aikin, za a hade shi ne da tashar jiragen ruwa da kuma tashar tsandauri da ke Zawaciki a jihar Kano domin saukaka shigowa da fitar da kaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel