Kwanaki 4 da Mutuwar Basarake Mai Daraja Ta 1, Masu Neman Sarauta 5 Za Su Fafata

Kwanaki 4 da Mutuwar Basarake Mai Daraja Ta 1, Masu Neman Sarauta 5 Za Su Fafata

  • Masu nadin sarauta a masarautar Ningi sun rubuta wasiku ga masu sha'awar neman kujerar marigayi Sarkin Ningi
  • Gwamnatin jihar Bauchi ce ta ba da umarni ga masu nadin sarautar da su fara shirin neman wanda zai gaji marigayin
  • Akalla 'ya'yan sarki biyar ake sa ran za su nemi sarautar, daga bisani za a tantance tare da tura sunayen wurin gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Kwanaki hudu bayan rasuwar Sarkin Ningi, Yunusa Muhammad Danyaya, an fara zawarcin kujerar sarautar.

Masu nadin sarauta sun tura wasika ga gidaje uku da ke da hurumin neman sarautar Ningi.

An fara shirin neman sarautar Ningi kwanaki 4 bayan rasuwar basarake
Masu nadin sarauta sun fara shirin zabar sabon Sarkin Ningi bayan rasuwar Alhaji Yunusa Danyaya. Hoto: Ibrahim Malam Goje.
Asali: Facebook

Ningi: An aika wasiku zuwa gidajen sarauta 3

Kara karanta wannan

An yi jana'izar surukar Ribadu: Atiku, Ganguje da wasu jiga jigan APC sun halarta

Gidajen sun hada da Gidan Mallam Hamza da Gidan Abubakar Danmaje da kuma Gidan Usman Danayaya, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wasikun, ana gayyatar gidajen guda uku domin neman sarautar Ningi idan suna da sha'awa.

Gwamnatin jihar Bauchi ta umarci masu nadin sarautar da su fara shirin zabar sabon sarki da zai jagoranci garin Ningi.

Za a fara karbar takardun masu sha'awar neman sarautar a yau Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 da misalin karfe 6.00 na yamma.

Masu nadin sarautar daga bisani za su tantance tare da tura sunayen mutane uku wurin Gwaman Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Daga nan ne kuma gwamnan zai yi amfani da ikonsa wurin zabar sabon sarkin daga cikinsu.

Wadanda ake tsammanin su nemi sarautar Ningi

Akalla akwai 'ya'yan masarautar biyar da ake sa ran za su nemi sarautar da suka hada da Alhaji Yusuf Yunusa Danyaya (Danburan Ningi) da Haruna Yunusa Danyaya (Chiroman Ningi).

Kara karanta wannan

Nuhu Ribaɗu ya yi babban rashi, Allah ya yiwa surukarsa rasuwa a Abuja

Sauran sun hada da Alhaji Abdullahi Ibrahim Gurama(Danlawal Ningi) da Alhaji Auwalu Isah (Danmajen Ningi) da kuma Alhaji Zakarai Isa (Santurakin Ningi).

Sanusi II ya yabawa halin marigayi Sarkin Ningi

Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yabawa marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.

Muhammadu Sanusi II ya ce marigayin na daya daga cikin sarakuna da suka nuna damuwa lokacin da ya shiga matsala a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.