Gwamnan Gombe Ya Kawo Tsari, Almajirai Za Su More Kamar Ma'aikatan Gwamnati

Gwamnan Gombe Ya Kawo Tsari, Almajirai Za Su More Kamar Ma'aikatan Gwamnati

  • Gwamnatin jihar Gombe ta fara shirin inganta lafiyar daliban tsangaya ta hanyar sa su a karkashin tsarin inshora
  • Yanzu haka gwamnatin ta sanya almajirai akalla 1000 a tsarin inshorar lafiya a kokarin tabbatar da daidaito
  • Ana sa ran yaran za su rika samun kulawa a fannin kiwon lafiyarsu, musamman idan bukatar hakan ta taso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta sanya daliban tsangaya akalla 1000 a tsarin inshorar lafiya domin saukaka masu samun kula da lafiyarsu.

Gwamnati ta ce ta bijiro da shirin ne domin tabbatar da cewa masu raunin cikin al'umar jihar sun samu damar kula da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Yayin da ambaliya ke rusa gidajen Kaduna, gwamnatin Uba Sani za ta gina sabon birni

Gombe
An sa almajirai 1000 a tsarin inshorar lafiya a Gombe Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa yayin kaddamar da shirin, mataimakin gwamnan Gombe, Dr Manassah Jatau ya ce wannan alama ce ta son inganta rayuwar al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Manassah Jatau ya kara da cewa shirin Gohealth da gwamnatin ta kirkiro, zai taimakawa wadanda ba su da hanyar kula da lafiyarsu.

Muhimmancin shirin inshorar lafiya a Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta ce shirin tsarin inshorar lafiya a jihar ya na da.muhimmancin gaske.

Jaridar Punch ta wallafa cewa mataimakin gwamna, Dr Manassah Jatau ya ce da gwamnati ba ta samar da shirin ba, yawa daga talakawan jihar ba za su iya ganin likita ba.

Dalilin gwamnatin Gombe na kawo tsarin lafiya

Gwamnatin Gombe ta ce ta gano almajirai na cikin barazanar kamuwa da cututtuka da yada su a tsakaninsu.

Dr. Manassah Jatau ya ce wannan na daga cikin dalilan da gwamnati ta sa su a cikin tsarin inshorar lafiya domin saukaka masu.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Tinubu na mayar da mu baya," Atiku ya fadi illar kayyade shekarun gama sakandare

Za a sa almajirai a inshorar lafiya

A baya kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta bayyana shirinta na inganta lafiyar almajirai ta hanyar sanya su a tsarin inshorar lafiya, ana sa ran almajirai da dama za su mori shirin.

A cewar shugaban shirin lafiya na Gohealth, Dr. Abubakar Musa gwamnatin jihar na da tsare-tsaren inganta lafiyar jama'ar Gombe, musamman marasa karfi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.