Ambaliyar Ruwa: Tinubu Ya Yi Alhinin Asarar da Aka Yi, Ya Dauki Alkawari
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan ambaliyar ruwan da aka samu a wasu daga cikin jihohin ƙasar nan
- Shugaba Tinubu ya bayyana alhininsa kan asarar rayuka da dukiyoyin da aka samu a sakamakon ambaliyar ruwan
- Tinubu ya yi alƙawarin ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ta shafa domin ganin sun farfaɗo daga asarar da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya nuna alhininsa ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya ce ya ƙudiri aniyar bayar da tallafin da ya dace domin ganin sun farfaɗo daga asarar da suka yi sakamakon ambaliyar ruwan.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya dauki alƙawari
Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin cewa hukumomin da abin ya shafa za su riƙa yin gargaɗi kan lokaci domin taimakawa wajen rage illar da ambaliyar ruwan ke jawowa.
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya samu labarin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yiwa al’umma da gonaki a faɗin ƙasar nan cikin tsananin baƙin ciki."
"Shugaban ƙasa ya jajantawa duk waɗanda wannan bala’i ya ritsa da su, musamman iyalan waɗanda suka mutu, manoma, al’ummomin da suka rasa matsugunansu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi."
"Shugaban ƙasan ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka mutu, tare da tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa, ta hannun hukumomin da abin ya shafa, za ta ci gaba da bayar da tallafin da ake buƙata ga mutanen da abin ya shafa."
- Ajuri Ngelale
Ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a Najeriya
A makon da ya gabata ne hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa ta auku a jihohi 27, inda ta shafi mutane 227,494 tare da lalata gidaje 32,837.
Hukumar NEMA ta kuma bayyana cewa ambaliyar ta lalata kadada 16,488 na gonaki da amfanin gona.
An buƙaci Tinubu ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa matasan ƙabilar Ijaw a ƙarƙashin ƙungiyar Ijaw Youth Council (IYC), sun nemi Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi murabus daga muƙamin ministan man fetur.
Matasan sun buƙaci Shugaba Tinubu ya naɗa tsayayyen wanda zai ci gaba da jagorantar ma'aikatar bayan ya yi murabus daga kan kujerar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng