Sanusi II Ya Fadi Basarake 1 da Ya Nuna Damuwa kan Halin da Ya Shiga a 2020

Sanusi II Ya Fadi Basarake 1 da Ya Nuna Damuwa kan Halin da Ya Shiga a 2020

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar ta'aziyya fadar marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya
  • Sanusu II ya ce tabbas an yi rashin mutumin kirki wanda yana daga cikin wadanda suka nuna damuwa bayan ya shiga wani hali
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake jimamin rasuwar basaraken da ya rasu a ranar Lahadi 25 ga watan Agustan 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yabawa marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.

Muhammadu Sanusi II ya ce marigayin na daya daga cikin sarakuna da suka nuna damuwa lokacin da ya shiga matsala a Kano.

Sanusi II ya yi alhinin rasuwar Sarkin Ningi, Yunusa Danayaya
Sarki Muhammadu Sanusi II ya tura sakon ta'aziyya game da rasuwar Sarkin Ningi, Muhammad Yunusa Danyaya. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Ibrahim Mallam Goje.
Asali: Facebook

Sarkin Ningi: Sanusi II ya yi ta'aziyya

Kara karanta wannan

"Sanusi II ne madubinmu" Sanata ya fadi abin da ya kamata Arewa ta yi da hikimominsa

Basaraken ya bayyana haka ne a wani bidiyo yayin ziyarar ta'aziyya ga masarautar Ningi bayan rasuwar sarki kamar yadda shafin @SanusiSnippets ya wallafa a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II ya nuna alhini game da rasuwar marigayin Mai Martaba Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya inda ya ce an yi babban rashi.

"Kan abin da ya faru, mutane da dama sun kira ni kan cewa abin da aka yi bai dace ba."
"Amma mutumin da ko kuma sarki da zai fito a jarida ya ce wannan abin da aka yi zalunci ne ba a kyauta ba sai Sarkin Ningi."

Sanusi II

"Sarkin Ningi mutumin kirki ne" - Sanusi II

"Ba za mu manta da wannan ba, ko wannan kadai ya isa mu yi rashinsa saboda bature na cewa kada ka mata mutane biyu, mutumin da ya tsaya da kai lokacin da kake cikin matsala da wanda ya juya maka a yayin da kake cikin matsala."

Kara karanta wannan

Kano: an barke da zanga-zanga da wakilin Sanusi II ya kori dagatai 3 babu dalili

- Muhamadu Sanusi II

Muhammadu Sanusi II ya ce tabbas ba zai manta da Sarkin Ningi ba da sauran wadanda suka nuna musu damuwa.

Sanata Ningi ya yabawa Sarki Sanusi II

Kun ji cewa Sanata Abdul Ningi ya fadi darussan da 'yan Arewa za su koya daga rayuwar Sarki Muhammadu Sanusi II.

Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Arewa ya ce shawarwarin Sarkin za su taimaka wurin dakile matsalolin Arewacin Najeriya.

Ya ce Sanusi II mutum ne mai ilimi da ya kamata a yi amfani da kwarewarsa wurin tabbatar da dakile matsalolin yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.