Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga a Kaduna, Sun Cafke Mai Ba Su Bayanai

Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga a Kaduna, Sun Cafke Mai Ba Su Bayanai

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri a ƙauyen Kurmin Kare da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna
  • Sojojin sun hallaka wasu ƴan bindiga biyu bayan sun ritsa su a cikin daji sakamakon samun bayanan sirri da suka yi a kansu
  • Jami'an tsaron sun samu bayanan sirri kan ƴan bindigan ne bayan sun cafke wani da ake zargi da laifin taimaka masu da bayanai
  • Hakan ta faru ne lokacin da wannan mutumi ya je siyo masu kayan abinci da magunguna a kasuwa da nufin ya mika masu a jeji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojoji sun hallaka wasu da ake zargin ƴan binidiga ne mutum biyu a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bayyana dalilin janyewa daga yankunan da ke fama da 'yan bindiga

Sojojin sun kuma cafke wani mai ba su bayanai a ƙauyen Kurmin-Kare cikin ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Sojoji sun yi nasara kan 'yan bindiga a Kaduna
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda sojoji suka kashe ƴan bindiga

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani shugaba a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar mata da aukuwar lamarin a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 3:00 na rana biyo bayan cafke mai ba ƴan bindigan bayanai a kasuwar Katari inda yaje siyan kayan abinci da magunguna ga ƴan bindigan.

Shugaban ya ce sojoji sun samu bayanai kan hakan, sai suka bi sawun wanda ake zargin tare da cafke shi, sannan ya kai su wurin da ƴan bindigan suka shirya karɓar kayayyakin.

"A wurin da ƴan bindigan suka shirya karɓar kayan abincin da magunguna, sojoji sun buɗe musu wuta inda suka hallaka mutum biyu daga cikinsu."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun hallaka jami'in tsaro, ,sun sace manoma

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, kan lamarin ba.

Ƙoƙarin jin ta bakinsa ya ci tura domin lokacin da aka kira wayarsa ba a same shi ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun harbe wani ɗan banga mai suna Saleh Aliyu a gonarsa a Kaduna.

Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu manoma huɗu a ƙauyen Nasarawar Azzara kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng