Hukumar DIA Ta Kama Ɗan Sanda da Wasu Mutane 19 Bisa Zargin Ta'addanci a Najeriya
- Hukumar tattara bayanan sirri DIA za ta ci gaba da tsare ɗan sanda da wasu da ake zargi da taimakawa ƴan ta'adda a Najeriya
- Wata babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ce ta amince DIA ta ci gaba da tsare waɗanda ake zargi na tsawon kwanaki 30
- Mai shari'a Peter Lifu ya yanke wannan hukunci a karar da hukumar DIA ta shigar ta hannun lauyanta watau S.A Aminu Esq.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba hukumar leken asiri (DIA) ta ƙasa izinin ci gaba da tsare wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) A. A. Babangida da wasu mutane 19.
Kotun ta amince hukumar DIA ta tsare su ne bisa zargin suna da hannu a hare-haren ƴan bindiga, garkuwa da mutane da ayyukan ta'addanci.
Jerin waɗanda DIA ke zargi da ta'addanci
The Nation ta tattaro cewa sauran waɗanda aka kama baya ga ɗan sandan sun haɗa da Usman Idris, Abu Safiyanu, Alhassan Idris, Sahada Ishaka da Abubakar Bello.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran su ne Yahaya Abdullahi, Haruna Salisu, Mohammed Muazu, Nura Idris, Alhaji Manu Mohammed, Umar Lamu da wani Abubakar Mandara.
Har ila yau akwai Suleiman Mohammed, Alhaji Madayi, Alhaji Amodu Oghewe da Uzoma Aghaoyibo.
Mai shari’a Peter Lifu ya yanke wannan hukuncin ne a karar da DIA ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1146/2024 ta hannun lauyanta S.A Aminu.
Kotu ta yanke hukunci kan bukatar DIA
Kotun ta umarci DIA ta ci gaba da tsare ASP Babangida da sauran waɗanda ake zargi na tsawon kwanaki 30 don ba jami’an tsaron damar kammala binciken da suke yi.
Hukumar DIA ta bayyana cewa ta kama ɗan sandan ne tun a watan Yuni kuma har yanzun yana tsare a hannunta.
Ta kuma zargi dan sandan da taimakawa ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga da ‘yan kungiyar ISWAP wajen gudanar da ayyukan ta’addanci a sassan kasar nan.
DIA ba ta samu yadda ta so a kotu ba
Tun farko dai lauyan hukumar leƙen asiri DIA, Aminu ya buƙaci kotu ta amince a ci gaba da tsare waɗanda ake zargin na tsawon watanni uku.
Mai shari’a Lifu ya ki amincewa da bukatar kwanaki 90 saboda wadanda ake zargin sun shafe watanni uku a tsare, kamar yadda Punch ta kawo.
Janar Musa ya kai ziyara Nijar
A wani rahoton kuma babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ziyarci takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Janar Mousa Barmo.
Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya sanar da haka ga manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng