Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito

  • Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ziyarci takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Janar Mousa Barmo
  • Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya sanar da haka ga manema labarai a Abuja
  • Wannan ziyara na zuwa ne bayan Jamhuriyar Nijar karkashin sojojin da suka yi juyin mulki sun fice daga ƙungiyar ECOWAS

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niamey, Niger - Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gana da takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Janar Mousa Barmo.

Wannan ziyara na zuwa ne bayan gwamnatin Sojin Nijar ta fice daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS).

CDS Musa da Janar Mousa.
Babban hafsan tsaron Najeriya, CDS Musa ya gana da takwaransa na Nijar Hoto: @Opebee
Asali: Twitter

Masani kuma mai sharhi da bibiyar harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya tabbatar da hakan a shafinsa na manhajar X ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya tafka asara, daruruwan 'yan APC sun watsar da ita ana daf da zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Musa dai ya kai ziyara Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar kuma ya samu tarba daga babban hafsan tsaron Nijar, The Cable ta ruwaito.

Hafsun tsaro na ƙoƙarin haɗa ƙasashen ECOWAS

A kwanakin baya, Janar Musa wanda shi ne shugaban kwamitin hafsoshin tsaron ECOWAS, ya yi kira ga ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar su dawo cikin ƙungiyar.

Babban hafsan tsaron Najeriya ya bayyana muhimmancin dawowar ƙasashen uku a kokarin da ake na magance matsalar tsaro, musamman ƴan tada ƙayar baya.

Meyasa hafsun tsaron ya ziyarci Nijar?

Ana ganin wannan ziyara na iya zama ta rarrashi da neman sulhu yayin da Janar Musa ke kokarin dawo da ƙasashen uku zuwa cikin ECOWAS.

Kungiyar ECOWAS dai na ci gaba da lallabar kasashen su dawo cikin inuwarta domin a haɗu a tunkari ƙalubalen tsaro a yammacin Afirka.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya haɗa kai da gwamna, sun shirya babban taron masu ruwa da tsaki a LP

Har yanzu dai ba a bayyana sakamakon ziyarar ba, amma hakan na nuni da wani mataki na warware takaddamar diflomasiyya da tunkarar kalubalen yankin.

Hafsoshin tsaron ECOWAS sun gana a Abuja

A wani rahoton kun ji cewa hafsoshin tsaro na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun gana a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Janar Christopher Musa.

Taron wanda ya gudana a hedkwatar tsaro ta kasa ya samu halartar duka hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka ban da na ƙasashe uku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262