Shugaban Majalisa Ya Gano Hanyar Magance Rikicin Manoma da Makiyaya
- Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa sauyin yanayi ya ta'azzara rikicin manoma da makiyaya
- Rt. Hon. Abbas ya bayyana haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki wanda kwamitin muhalli na majalisa ya shirya
- Ya bayyana cewa dole ne a dauki dabarun zamanantar da kiwo da noma domin rage rikici tsakanin masu noma da kiwo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Benue - Kakakin majalisar wakilai, Hon.Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa karuwar sauyin yanayi ya kara jawo rikicin manoma da makiyaya a kasar nan.
Kakakin ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki inda aka nuna wani shirin fim kan sauyin yanayi da rikicin manoma da makiyaya a jihar Binuwai.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Hon. Tajuddeen Abbas ya samu wakilcin dan majalisa mai wakiltar Makurdi/Guma a jihar Binuwai, Hon. Dickson Takighir.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yadda ake cigaba da amfani da tsofaffin dabarun kiwo na daga cikin matsalolin da ke jawo saɓani tsakanin manoma da makiyaya.
Hanyar magance rikicin manoma da makiyaya
Majalisar wakilai ta bayyana cewa dole a zamanantar da noma da kiwo domin magance matsalar da ake samu tsakanin masu sana'ar biyu.
Voice of Nigeria ta wallafa cewa kakakin majalisa, Tajuddeen Abbas da ya bayyana haka, ya ce sai manoma da makiyaya sun yi koyi da tsarin cigaba domin bunkasa sana'o'insu.
Ana son magance rikicin manoma da makiyaya
Kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya ce gwamnatin tarayya da majalisa na son magance rikicin manoma da makiyaya.
Ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta samar ma'aikatar kula da dabbobi domin zamanantar da kiwo.
Fada ya barke tsakanin manoma da makiyaya
A baya mun ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin manoma da.makiyaya bayan zargin an kashe wani manomi a Gbagyi a karamar hukumar Bosso da ke Neja.
An ce makiyayan sun kashe manomin ne bayan ya yi masu magana kan barin dabbobinsu sakaka a cikin gonarsa, lamarin da ya sa mazauna Gbagyi su ka yi ramuwar gayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng