DSS: Jaafar Jaafar Ya Tona Illar da Bichi Ya Yi a Hukumar, Ya Zargi Matarsa
- Fitaccen dan jarida, Jaafar Jaafar ya fadi illar da tsohon shugaban DSS, Yusuf Bichi ya yi ga hukumar lokacin shugabancinsa
- Jaafar ya zargi Bichi da rikita tsarin daukar aiki a hukumar inda ya ke daukar wadanda suka kammala karatu a jami'o'in Cotonou
- Dan jaridar ya nuna damuwa kan yadda Bichi ya bar matarsa ke shiga lamarin daukar aiki da karin girma a hukumar tsaron
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Fitaccen dan jarida da ke zama a Birtaniya, Jaafar Jaafar ya caccaki tsohon shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi.
Jaafar ya zargi Bichi da lalata hukumar tare da zama hukumar tsaro ta 'yan APC zalla a Najeriya.
DSS: Jaafar Jaafar ya dira kan Bichi
Dan jarida, Jaafar ya bayyana haka a shafinsa na X a yau Laraba 28 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaafar ya zargi Bichi da lalata tsarin daukar aiki a hukumar wurin nuna wariya da rashin bin ka'idar daukar aiki.
Ya ce mafi yawan wadanda ake dauka ba za su iya haye jarabawar da ake yi wa masu tsaro a kamfanoni masu zaman kansu ba.
"Tsohon shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi ya lalata tsarin daukar aiki a hukumar wurin kin bin ka'idoji inda ake daukar wadanda ba za su iya ko nasara a jarabawar daukar jami'an tsaro a kamfanoni masu zaman kansu ba."
"Bichi ya dauki mafi yawan wadanda suka gama karatu a jami'o'in Cotonou da kuma kara wa'adin daraktoci da suka yi ritaya inda hakan ke kashe guiwar masu tasowa."
"Ya bar matarsa tana katsalandan a harkar daukar aiki a hukumar da kuma karin girma, ta kware wurin cin zarafin mutane a kan hanya da fada da yan siyasa da ke bangaren adawa."
- Jaafar Jaafar
Musabbabin murabus din Bichi a DSS
Kun ji cewa rahotanni sun bayyana musabbabin shirin korar tsohon daraktan hukumar DSS, Yusuf Bichi da shugaban kasa ya yi.
Wata majiya ta tabbatar da cewa Bichi ya yi murabus ne saboda ba su ga maciji da mai ba da shawara a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng