An Shiga Jimami Yayin Jana'izar Sojan Najeriya da Ya Rasu Wajen Ceto Mutane

An Shiga Jimami Yayin Jana'izar Sojan Najeriya da Ya Rasu Wajen Ceto Mutane

  • An yi jana'izar Laftanal Kwamanda Gideon Yashim Gwaza, wanda ya rasu yayin ceto mutane 59 da ke daf da nutsewa a ruwa a jihar Rivers
  • Sojan ruwan da ya ceto mutanen a Okpobo da ke jihar Rivers, an yi jana'izarsa ne ranar Laraba a maƙabartar sojoji da ke birnin tarayya Abuja
  • Da yake magana wajen jana'izar, wani jami'i, ya bayyana marigayin a matsayin jami'i mara tsoro wanda ke gudanar da aikinsa bisa sadaukarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An yi jana'izar jami'in sojan ruwan Najeriya Laftanal Kwamanda Gideon Yashim Gwaza, wanda ya rasu a jihar Rivers.

An yi jana'izar marigayin ne bayan ya rasa ransa yayin ceto wasu mutane da jirgin ruwansu yayi yunƙurin nutsewa a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

An yi jana'izar sojan Najeriya
An binne sojan ruwan Najeriya a Abuja Hoto: Nigerian Navy
Asali: Twitter

An birne sojan ruwan Najeriya

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an yi jana'izar marigayin ne a ranar Laraba, 28 ga watan Agustan 2024 a maƙabartar sojoji da ke birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin ceton ne dai ya sanya an yi nasarar ceto mutane 59 daga jirgin ruwan mai suna MV AMBIKA 4, wanda ya kusa nutsewa a cikin kogin Okpobo da ke jihar Rivers

Marigayin dai ya rasa ransa ne a ranar, 30 ga watan Yulin 2024 a wajen ƙoƙarin ceto mutanen.

Sojan ya samu shaida mai kyau

Jaridar Leadership ta ce da yake magana a wajen jana'izar, kwamandan rundunar sojojin ruwa da ke Bonny, Kyaftin M.A Mohammed ya bayyana cewa marigayin ya san cewa akwai hatsari sosai, amma ya sadaukar da ransa domin ceto mutanen.

Ya ƙara da cewa marigayin ya sha nuna rashin tsoro a yayin gudanar da ayyukan ceto masu hatsari.

Kara karanta wannan

Jigawa: Mai shayi ya lakaɗawa matashi duka har lahira kan ɓatan Indomi da Burodi

"Bayan rasuwarsa, wasu mutum biyu mazauna Bonny sun gaya mani yadda ya ceto su shi kaɗai a daren. Ko a baya na sha ganin yana nuna rashin tsoro a wurare da dama."
"Yana yin dukkanin aikin da aka ba shi cikin himma da sadaukar da kai."

- Ƙyaftin M.A Mohammed

Tsohon hafsan soja ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, ɗan asalin jihar Kogi, Admiral Ibrahim Ogohi ya rasu yana da shekaru 76.

Wata majiya daga iyalan marigayin ta ce tsohon hafsan tsaron na Najeriya ya rasu ne a asibiti sakamakon jinya da ya daɗe yana fama da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng