Yadda Soja Ya Harbe Ɗan Tsohon Shugaban Sojoji, Ya Sace Motarsa a Abuja
- Wani sojan saman Najeriya, Abdulrashid Muhammad ya fadi yadda ya kashe dan tsohon shugaban sojojin ruwan Najeriya
- Abdulrashid Muhammad ya bayyana yadda dan mai gidan nasa ya nemi taimakon ya raka shi a lokacin da zai fita zuwa wani waje da dare
- Kwamishinan yan sanda a birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa Abdulrashid Muhammad ya sace motar wanda ya kashe din
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar yan sanda ta gurfanar da wani sojan saman Najeriya da ake zargi da kisan dan tsohon shugaban sojoji.
An dauki sojan mai suna Abdulrashid Muhammad aikin ba da tsaro a gidan tsohon shugaban sojojin saman Najeriya, VA I.I Ibrahim (Mai ritaya).
Jaridar Punch ta wallafa cewa sojan ya amsa laifin kashe yaron gidan da aka tura shi aikin da sace motar hawansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soja ya amsa laifin kisan kai
Sojan saman Najeriya, Abdulrashid Muhammad ya amice da cewa ya kashe matashi mai suna Aminu, ɗa ga tsohon shugaban sojojin ruwan Najeriya.
Rundunar yan sanda ta gurfanar da Abdulrashid Muhammad a gaban alkali domin masa hukunci kan laifin.
Yadda sojan Najeriya ya kashe Aminu
Daily Trust ta ruwaito cewa Abdulrashid Muhammad ya bayyana cewa wata rana da misalin karfe 11:30 na dare Aminu ya bukaci ya raka shi zuwa wani waje.
Bayan Aminu ya je zai cire kudi domin sayen wani abu ne Abdulrashid Muhammad ya ce ya harbe shi kuma ya mutu har lahira.
Dalilin da yasa soja ya kashe Aminu
Yayin da yake amsa tambayoyi, Abdulrashid Muhammad ya bayyana cewa ya kashe Aminu ne domin ya tafi da motarsa.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta kwato mota kirar Prado da Abdulrashid ya sace bayan kashe Aminu.
Sojoji sun gwabza da yan bindiga
A wani rahoto, kun ji cewa yan bindiga sun kai hari kan sojojin Najeriya, sun kashe soja tare da mutane da yawa a kananan hukumomi biyu a jihar Benuwai.
Kwamandan rundunar OPWS, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya tabbatar da kashe sojan, amma ya ce dakarun sun halaka yan bindiga uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng