Kano: NSCDC Ta Hannatawa Kotu da NCC Kayayyakinsu da Aka Sace Lokacin Zanga Zanga

Kano: NSCDC Ta Hannatawa Kotu da NCC Kayayyakinsu da Aka Sace Lokacin Zanga Zanga

  • Hukumar tsaron farar hula ta reshen Kano ta mika kayayyakin sata da ta kwato a lokacin zanga-zangar yunwa ga masu su
  • Wata sanarwar da kakakin hukumar, Ibrahim Abdullahi ya fitar ta nuna cewa kayayyakin mallakin NCC ne da kotun Kano
  • Kayayyakin sun hada da Cisco Switch guda biyu da kudinsu ya haura N400m, na’urorin kwamfuta da dai sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Jami’an tsaron NSCDC sun mika kayayyakin da wasu 'yan baranda suka sace a yayin zanga-zangar yaki da yunwa da aka yi a jihar Kano ga masu su.

An mika kayayyakin satar na miliyoyin Naira ga masu su; hukumar NCC da kuma babbar kotun jihar Kano a hedikwatar NSCDC a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

NSCDC ta yi magana kan kayayyakin sata da ta kwato daga barayi a lokacin zanga zanga
Kano: NSCDC mayar da kayayyakin da ta kwato hannun 'yan baranda suka sace a NCC da kotun jiha. Hoto: @The_HBMayana
Asali: Twitter

NSCDC ta mika kayayyakin sata

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mista Ibrahim Abdullahi ya fitar, a cewar rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Kayayyakin sun hada da Cisco Switch guda biyu da kudinsu ya haura N400m, na’urorin kwamfuta, na’urorin sanyaya iska.
"Sauran kayayyakin sun hada da kujerun alfarma, kofofi/taga, na’urar kwafar takardu da kuma littattafan shari’a da sauransu.
"Wadannan kayan aikin mallakin cibiyar masana'antu ta NCC da ke Kano ne da kuma babbar kotun jiha dake a harabar sakatariyar Audu Bako."

- A cewar sanarwar Mista Ibrahim.

NCC, kotu sun jinjinawa NSCDC

Ya yi bayanin cewa, jami’an hukumar na sashen CNAI suka samu nasarar kwato kayayyakin jim kadan bayan da wasu 'yan baranda suka yi awon gaba da su a lokacin zanga-zanga.

Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito Aminu Chido, da yake karbar kayayyakin a madadin hukumar NCC ta Kano, ya jinjina tare da yabawa kokarin da jami’an NSCDC na kwato kayan.

Kara karanta wannan

Magani na gagarar talaka: Masu ciwon sukari sun nemi alfarma wajen Shugaba Tinubu

Har ila yau, babbar kotun jiha ta Kano wadda ma’aikatanta suka karbi kayayyakin a madadinta ta yabawa jami’an hukumar bisa nuna kishin kasa.

Bidiyo: Masu zanga zanga na sata

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda ta saki wani bidiyo da ya ke nuna lokacin da wasu 'yan baranda ke satar dukiyar jama'a a Kano.

Rundunar ta ce ta samu nasarar kwato wasu daga cikin kayayyakin da 'yan barandan suka sata yayin zanga-zangar, tare da kuma fara bi gida gida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.