TSA: Abba Ya Sa a Rufe Dukkanin Asusun Bankin Hukumomi da Ma’aikatun Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin rufe dukkanin asusun banki na hukumomi da ma'aikatun jihar
- Babban mai tallafawa Gwamna Yusuf kan kafafen zamani, Hassan Sani Tukur ya sanar da hakan a ranar Laraba
- Tukur ya bayyana cewa gwamnan ya ba da umarnin ne a shirye-shiryen jihar na komawa amfani da asusun bai daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin mai girma Abba Kabir Yusuf ta sauya tsarin yadda za ta rika karba, ajiyewa da kuma rarraba kudin jihar.
Maimakon yadda aka saba na kowacce ma'aikata da hukuma ta rika amfani da asusunta, yanzu gwamnatin ta mayar da amfani da tsarin asusun bai daya.
Abba ya rufe asusun ma'aikatu
Babban mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai ga Gwamna Abba Yusuf, Hassan Sani Tukur ya sanar da hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hassan Tukur, a sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, 28 ga Agusta, ya bayyana cewa gwamnan ya ba da umarnin rufe asusun dukkanin ma'aikatu da hukumomin jihar.
Ya ce wannan matakin na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Kano na komawa amfani da asusun bai daya wajen hadar kudin jihar.
Kano: Amfani da asusun bai daya
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin rufe dukkanin asusun bankin da ma’aikatu da hukumomin jihar ke amfani da shi.
"Rufe asusun bankunan na daga shirye-shiryen fara gudanar da tsarin amfani da asusun ajiyar kuɗi na bai daya."
CBN zai rufe asusun jama'a
A wani labarin, mun ruwaito cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya sanar da cewa zai rufe dukkanin asusun bankin da ba a hada shi da lambobin BVN da NIN ba.
Matakin rufe asusun bankunan zai zama an hana kudaden cikin asusun fita har sai lokacin da wa'adin matakin zai kare ko kuma mai asusun ya sabunta bayanansa.
A yayin da wasu ke ganin hakan takura ce, bankin ya ce wannan mataki zai inganta harkokin kudade da kuma samar da tsaro a asusun bankunan jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng