Jami'an Tsaro Sun Kashe 'Dan Fashi, An Damke Mai Kai Kakin Sojoji ga Miyagu

Jami'an Tsaro Sun Kashe 'Dan Fashi, An Damke Mai Kai Kakin Sojoji ga Miyagu

  • Jami'an tsaron kasar nan sun kara samun nasara a yakin da su ke yi da miyagu a jihar Kaduna
  • Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar kashe wani dan fashi da makami a jihar
  • Jami'in hulda da jama'a na Kaduna, ASP Mansur Hassan ya tabbatar da cewa an kama mai safarar kakin sojoji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Rundunar yan sandan Kaduna ta bayyana samun nasara a kan wasu daga cikin miyagun da su ka addabi jihar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan ne ya tabbatar da cewa an cafke mai kai wa miyagu kakin sojoji a daji.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta sha alwashin ceto dukkanin mutanen da ke hannun miyagu

police
Yan sanda sun kama mai safarar kakin sojoji ga yan sanda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta bayyana cewa mutumin na kai wa miyagun yadin, su kuma miyagun su na dinkawa da kansu a wani daji da ke Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama mutumin a hanyar zuwa Birnin Bwari, inda aka gan shi da kakin sojoji na mutum 15 da miyagun za su yi amfani da su wajen cin zalin jama'a

Kaduna: Yadda aka kama dan aiken miyagu

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami'anta da ke sintirinsu ne su ka kama mutumin da kakin sojojin kulle a cikin bakar leda, Thisday ta wallafa.

Mutumin ya shaidawa jami'an tsaro cewa zai kai kakin zuwa Chukuma a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, inda su kuma miyagun za su dinka.

'Yan sanda sun kashe dan fashi a Kaduna

'Yan sanda a jihar Kaduna sun yi nasarar kashe wani dan fashi da makami a daidai lokacin da su ka cafke mai safarar yadin kakin sojojin.

Kara karanta wannan

Miyagu za su ga ta kansu, Rundunar yan sanda ta daukarwa yan Najeriya alwashi

Kakakin rundunar 'yan sandan Kaduna, ASP Mansur Hassan ya ce wanda aka kama ya na taimaka masu wajen bincike domin shaƙo sauran abokan aikinsa.

Sojoji sun hallaka miyagu a Kaduna

A wani rahoton kun ji cewa rundunar sojojin kasar nan ta samu nasarar hallaka dan ta'adda guda daya yayin da aka fatattaki miyagu a wani samame da su ka kai Kaduna.

Rundunar ta kara da cewa ta samu nasarar raunata 'yan ta'adda da dama, yayin da aka kwato tarin makaman da su ke amfani da shi wajen kai farmaki kan al'uma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.