"Gwamnatin Tinubu na Mayar da Mu Baya," Atiku Ya Fadi Illar Kayyade Shekarun Gama Sakandare

"Gwamnatin Tinubu na Mayar da Mu Baya," Atiku Ya Fadi Illar Kayyade Shekarun Gama Sakandare

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya caccaki kudurin gwamnatin tarayya kan gama sakandare
  • Atiku Abubakar da ke jam'iyyar hamayya ta PDP ya ce tsarin kayyade shekarun kammala sakandare bai kamata ba
  • 'Dan takaran na 2023 ya ce tsarin kamar mayar da kasar nan bayan ne kuma zai kawo cikas ga masu samun tallafin karatu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki matakin gwamnatin Bola Tinubu na kayyade shekarun kammala sakandare.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana cewa daga shekarar 2024, ba za a sake amincewa 'yan kasa da shekara 18 rubuta jarrabawar WAEC, NECO ko UTME ba.

Kara karanta wannan

Rikici na neman ruguza APC a jihar Arewa, jam'iyya ta kira taron gaggawa

Atiku
Atiku ya yi martani kan shirin Tinubu na kayyade shekarun gama sakandare Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya ce matakin zai mayar da kasar nan baya, inda ya zargi gwamnati da cewa ba ta san abin da ta ke yi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan takarar ya kara da cewa bai dace gwamnati ta yanke hukunci kai tsaye wajen kayyade shekarun daliban ba saboda illarsa ga ilimi.

Atiku ya fadi illar kayyade shekarun dalibai

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya ce kayyade shekarun daliban da za su rubuta jarrabawar kammala sakandare zai kawo cikas ga tallafin karatu.

Ya ce abin da ya fi dacewa shi ne gwamnatin tarayya ta bar jihohi su yanke irin wannan hukunci dai-dai da yadda ya dace da tsarinsu.

"Gwamnati ta nuna gazawa kan ilimi" - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa matakin da gwamnati ta dauka ya nuna gazawarta kan dalibai masu hazaka.

Kara karanta wannan

WAEC da NECO: Gwamnati ta hana 'yan kasa da shekaru 18 tafiya manyan makarantu

Atiku Abubakar ya ce matakin abin kunya ne kan masu basira a kasar nan, domin ya na nuna cewa gwamnati ba ta damu da su ba.

WAEC: Gwamnati ta kayyade shekarun dalibai

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga yanzu, ba za a kara barin 'yan kasa da shekaru 18 su rubuta jarrabawar kammala sakandare ko ta shiga jami'a ba.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka ya ce matakin ba sabo ba ne, kuma za a cigaba da amfani da shi a shekarar 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.