Rundunar Yan Sanda Ta Sha Alwashin Ceto Dukkanin Mutanen da ke Hannun Miyagu

Rundunar Yan Sanda Ta Sha Alwashin Ceto Dukkanin Mutanen da ke Hannun Miyagu

  • Rundunar yan sandan kasar nan ta sake daukar alkawarin kawo karshen satar mutane a fadin kasa
  • Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ne ya dauki alkawarin lokacin da ya ke yabon yadda aka ceto dalibai
  • Kayode Egbetokun ya yi alkawarin cewa za a ceto dukkanin mutanen da ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sandan kasar nan ta sake daukar alkawarin ceto dukkanin mutanen da miyagu su ka sace a sassan Najeriya.

Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ne ya sha alwashin a lokacin da ya ke yabawa jami'ansa kan jajircewarsu wajen ceto likitoci dalibai 20 daga hannun miyagu.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin makiyaya da manoma a Arewacin Najeriya, an kashe mutum

Police
Yan sanda sun yi alkawarin ceto dukkanin mutanen da yan bindiga su ka sace Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa babban Sufeton ya ce daga yanzu ba za su huta ba, har sai an tabbatar da kwato mutanen da ke tsare a maboyar miyagu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci hadin kai daidaikun jama'a da kungiyoyi wajen ganin an cimma manufar kakkabe rashin tsaro

Yan sanda sun nemi hadin kan jama'a

Rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayyana muhimmancin samun hadin kan jama'a wajen raba kasar nan da ayyukan ta'addanci, Jaridar Punch ta wallafa labarin.

Babban Sufeton 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya kuma shawarci jama'a su rika shiga al'amuran tsaro domin tabbatar da tsare rayukansu

Yan sanda sun yaba da kokarin NSA

Rundunar 'yan sanda ta yaba da jajircewar ofishin mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro (NSA), wajen dakile ayyukan ta'addanci a kasar nan.

Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ya ce ofishin NSA na ba su hadin kai wajen tabbatar da ya sauke nauyin tsaron rayukan jama'a da ya rataya a wuyansa.

Kara karanta wannan

"Ba mu da labari," Ƴan sanda su yi magana kan sace mutane 150 bayan kisan Sarkin Gobir

Yan sanda sun musanta masaniyar sace mutane

A baya kun ji cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta ce ba ta da labarin miyagu sun kai hari Gobir, tare da sace mutane sama da 150 kwanaki kadan bayan kashe sarkin garin.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa'i ne ya bayyana haka, amma ya tabbatar da cewa yankin Gobir na fuskantar barazanar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.