NERC: Jihohi 6 da Gwamnatin Tarayya Ta Amince Su Kula da Kasuwancin Wutar Lantarki
- A ranar 27 ga Agusta ne NERC ta mika ragamar ikon gudanarwarta zuwa ga jihohi shida: Enugu, Ekiti, Ondo, Imo, Oyo da Edo
- Wadannan jahohin sun kafa nasu hukumomin kula da wutar lantarki domin sa ido da sarrafa kasuwanciann wutar a ykunannsu
- Hukumar NERC ta yi bayanin cewa canjin ya ba da dama ga jihohi su sarrafa tsarin lantarki a daidai da bukatun jama'arsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - ranar 27 ga Agusta, hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da cewa jihohi shida sun samu ikon sarrafa kasuwar wutar lantarki a hukumance.
Bayan mika ragamar ikon gudanarwar NERC, jihohin da suka hada da Enugu, Ekiti, Ondo, Imo, Oyo, da Edo yanzu za su rika kula da kasuwannin wutar lantarkinsu.

Source: Getty Images
Ba jihohi iko kan wutar lantarki
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar NERC ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce wadannan jihohin sun kafa nasu hukumomin kula da wutar lantarki domin gudanar da kasuwanci da kuma sa ido kan amfani da wutar.
Ana ganin wannan matakin a matsayin gagarumin sauyi a tsarin gudanarwar hukumar NERC, wanda ya ba da damar jihohi su sarrafa wutar lantarki a cikin yankunansu.
Duba sanarwar a kasa:
Kafa hukumar NERC a 2005
An kafa hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) a shekarar 2005 bayan amincewa da dokar kawo sauyi a bangaren wutar lantarki.
Babban aikinta shi ne tsara yadda ake samar da wutar lantarki, rarrabawa, da sayar da wutar a Najeriya.
An kafa NERC ne domin inganta ayyuka da tabbatar da kasuwar wutar lantarki ta gudana a kan madaidaiciyar turba da kuma magance kalubalen fannin wutar.
A tsawon shekarun nan, hukumar ta aiwatar da tsare-tsare daban-daban da nufin inganta ayyukan samar da wutar da kuma fadada hanyoyin samun wutar a fadin kasar.
NERC ta kara kudin wutar lantarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NERC ta kara kudin wuta ga abokan huldarta miliyan 1.9 dake sahun Band A bayan sauye-sauyen da aka samu daga janye tallafin lantarki.
Hukumar NERC ta sanar da kara kudin wutar ne da kusan kashi 230% ga anguwanni 481 da ke shan wutar na awanni 24, kamar yadda muka tattaro bayanin anguwannin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

