Tinubu Na Shirin Lulawa Kasar Waje, COAS Ya Yi Magana Mai Zafi Kan Masu Kiran Juyin Mulki
- Hafsan sojojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Taoreed ya ce sojoji ba za su yi sakaci a yi amfani da su wajen kifar da gwamnati ba
- COAS Lagbaja ya ce duk da wasu manyan mutane sun nemi sojoji su kwace mulki amma ba za su yarda su kara zubarwa da kansu ƙima ba
- Shugaban sojojin ya ƙara nanata cewa babu wani dalili da zai sa su yi ƙoƙarin ruguza mutunci da ƙimar da suka gina tsawon shekaru 25 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ce sojoji ba za su faɗa tarkon masu kiraye-kirayen juyin mulki ba.
Lagbaja ya bayyana cewa rundunar sojoji da za ta tsorata ko ta faɗa tarkon manyan masu faɗa a ji da ke kirayen-kirayen sojoji su karɓe iko da ƙasar nan.
Laftanar-Janar Lagbaja ya faɗi haka ne ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2024, a jawabinsa na bude taron babban hafsan sojin kasa na 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin ƙasa ba zasu karɓe mulki ba
Kamar yadda Daily Trust ta kawo, a wannan lokacin masu shirya taron sun haɗa karo na biyu da na uku a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da fafutukar dawo da martabarsu da suka rasa sakamakon ɗaukar shekaru da dama na mulkin soja.
Saboda haka a cewar COAS, dakarun sojoji ba a shirye suke su rusa ƙimar da suka samu suka gina ta tsawon shekaru 25 da suka wuce ba.
COAS ya aika sako ga masu son kifar da Tinubu
Lagbaja ya nuna rashin amince da kiraye-kirayen da ƴan Najeriya suka yi a lokacin zanga-zangar farkom watan Agusta cewa sojoji su karɓe ragamar mulki.
"Wani batu da ya taso a lokacin zanga-zanga shi ne kiraye-kirayen sojoji su ƙwace mulki da ƙarfin bindiga.
"A matsayina na hafsan sojoji, amsar da za mu bayar ita ce mun gode amma sojojin Najeriya ba za su bari a yi amfani da su wajen kifar da gwamnati mai ci ba," in ji Lagbaja."
DHQ ta jero nasarorin sojoji a mako 1
Kuna da labarin Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 171 tare da ceto mutane 134 da aka yi garkuwa da su a mako guda.
Hedkwatar tsaron ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa sojojin sun kwato manyan bindigu da alburusai daga hannun ƴan ta'adda.
Asali: Legit.ng