An Yi Jana’izar Surukar Ribadu: Atiku, Ganguje da Wasu Jiga Jigan APC Sun Halarta

An Yi Jana’izar Surukar Ribadu: Atiku, Ganguje da Wasu Jiga Jigan APC Sun Halarta

  • An yi jana'izar Hajiya Ummu Iya Abubakar, surukar mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu
  • An ruwaito cewa an yi sallar jana'izarta ne da misalin karfe 1:30 a babban masallacin Abuja awanni bayan sanar da rasuwarta
  • Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai Atiku Abubakar, Abdullahi Ganduje da Aliyu Modibbo da wasu jiga jigan APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da Abdullahi Ganduje, shugaban jam'iyyar APC mai mulki ta kasa sun halarci jana'izar mahaifiyar Malam Nuhu Ribadu.

An gudanar da Sallar Janai'zar Hajiya Ummu Iya Abubakar, surukar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da misalin karfe 1:30 a babban masallacin Abuja.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribaɗu ya yi babban rashi, Allah ya yiwa surukarsa rasuwa a Abuja

Atiku ya halarci jana'izar surukar Nuhu Ribadu, Ganduje da jiga jigan APC sun halarta
An yi jana'izar surukar Nuhu Ribadu, Atiku, Ganduje da wasu jiga-jigan APC sun halarta. Hoto: @AtikuMedia2023
Asali: Twitter

An yi jana'izar surukar Ribadu

Jaridar daily Trust ta ruwaito cewa daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman da takwaransa na gidaje da raya Birane, Arc Ahmed Dangiwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Sabon shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Mohammed Mohammed, da tsohon shugaban hukumar Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Tsohon ministan babban birnin tarayya, Dakta Aliyu Modibbo, na daga cikin wadanda aka ce sun halarci jana'izar Hajiya Ummu Iya.

Bayan sallar janaizarta, an binne ta a makabartar Gudu da ke Abuja.

Surukar Ribadu ta rasu

Mun ruwaito cewa surukar Ribadu ta rasu da sanyin safiyar Talata, 27 ga Agusta, 2024.

Amadadin iyalan Sanata (Farfesa) Iya Abubakar, muna alhinin sanar da ku rasuwar Hajiya Ummu Iya Abubakar (Babba) da sanyin safiyar yau Talata 27 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin rasuwar Sarkin Gobir, gwamnonin Arewa sun tura sako ga Sultan

“Allah SWT ya saka mata da dukkanin ayyukanta na alheri, ya gafarta mata zunubanta, ya haskaka kabarinta, ya sanyata a mafi daukakar gida a cikin Aljannah."

- A cewar wata sanarwa daga iyalanta.

Ribadu ya tilasta Bichi murabus?

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata majiya ta yi ikirarin cewa Yusuf Bichi ya yi murabus daga shugaban hukumar DSS ne saboda sabanin da ke tsakaninsa da Nuhu Ribadu.

Majiyar ta bada tabbacin cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai iya sallamar duk wanda ke kokarin kawo cikas ga mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Malam Ribadu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.