Ya Sha da Ƙyar: Bidiyon Fusatattun Matasa Sun Farmaki Ɗan Majalisar Tarayya a Bauchi

Ya Sha da Ƙyar: Bidiyon Fusatattun Matasa Sun Farmaki Ɗan Majalisar Tarayya a Bauchi

  • Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ningi/Warji a jihar Bauchi ya sha da ƙyar bayan harin da matasa su ka kai masa
  • Matasan sun zargi Hon. Adamu Hashimu Ranga da watsi da al'amuransu, yayin da ya ke morewa a Abuja
  • Matasan sun rika bin motar Hon Ranga a guje, duk da harbin bindiga da jami'an tsaro su ka rika yi domin korarsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ningi/Warji a jihar Bauchi ya tsallake rijiya da baya bayan matasan mazaɓarsa sun yi yunkurin kai masa hari.

Matasan sun farmaki motar Hon. Adamu Hashimu Ranga a ranar Lahadi yayin ta'azziyar da ya kai bisa rasuwar sarkin Ningi, Alhaji Muhammadu Yunusa Danyaya.

Kara karanta wannan

Jigawa: Mai shayi ya lakaɗawa matashi duka har lahira kan ɓatan Indomi da Burodi

Representatives
Matasa sun kai hari kan ɗan majalisarsu a Bauchi Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Bauchi: Yadda aka farmaki dan Majalisar Tarayya

A bidiyon da wani mai amfani da shafin Facebook, Sanusi Rabi'u Bala ya wallafa, an rika jiyo harbin bindiga domin tarwatsa masu ƙoƙarin kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin matasan na takaicin yadda ɗan majalisar na su ya yi watsi da su tun bayan zaɓarsa da su ka yi a shekarar 2023

Bauchi: Matasa sun fusata da ɗan majalisarsu

Matasan Ningi sun raka ɗan majalisarsu , Hon. Adamu Hashimu da duwatsu da ƙasa, yayin da su ke ihun "Ba ma yi, ba ma yi," a yammacin Lahadi.

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa matasan sun yi yunƙurin kai harin ne da karfe 5.42 na yamma bayan Hon. Ranga ya je ta'aziyyar rasuwar Sarkin Ningi.

Duk da yunkurin da aka yi na ba matasan haƙuri, sai da su ka fasa gilasan motar yayin da direbansa ya figi motar a guje domin samun mafaka.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun tono bama bamai a garuruwa da dama a Arewacin Najeriya

Kakakin Majalisa ya yi murabus a Bauchi Kakakin Majalisa ya yi murabus a Bauchi

A baya mun ruwaito cewa kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Babayo Akuyam da mataimakinsa Ahmed Abdullahi sun yi murabus.

Rt. Hon Akuyam da Hon. Ahmed Abdullahi sun yi murabus ne bayan dawowar tsohon kakakin majalisar Adamu Suleiman da mataimakinsa, Jamilu Ɗahiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.