Jigawa: Mai Shayi Ya Lakaɗawa Matashi Duka Har Lahira Kan Ɓatan Indomi da Burodi
- Wani mai shayi a kauyen Sararai da ke ƙaramar hukumar Dutse a Jigawa ya kashe matashi ɗan shekara 20 kan zargin satar indomi da burodi
- Ƴan sanda sun kama wanda ake zargi, Abdulrashibu Ya'u kuma ya amsa laifin, ya ce mamacin ya matsa masa da sata
- Makotan mai shayin sun bayyana cewa wanda ake zargin ya ɗaure matashin, ya riƙa bugunsa da itace har sai da ya daina motsi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Wani mai shayi ɗan kimanin shekara 40 a duniya, Abdulrashibu Ya’u, ya yiwa wani matashi dukan tsiya har lahira a jihar Jigawa.
Lamarin ya auku ne a kauyen Sararai da ke yankin Jigawar Tsada a ƙaramar hukumar Duts a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa an zargi mamacin mai suna, Hassan Garba, ɗan shekara 20 da satar burodi, madara, indomi da kuma man fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigawa: Yadda mai shayi ya yi kisa
Wannan ya sa mai shayin ya ɗaure matashin, ya dinga bugunsa da icce har sai da ya mutu, kamar yadda Punch ta tattaro.
Take bayan samun rahoton, ƴan sanda suka kai ɗauki wurin, suka kama wanda ake zargi kana suka garzaya da Hassan Asibiti, daga zuwa likitoci suka ce ya mutu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da lamarin yayin hira da ƴan jarida a Dutse.
Wane mataki ƴananda suka ɗauka?
Ya ce Abdulrashibu Ya’u ya amince da aikata laifiin, inda ya ce yawan sace-sacen da Hassan ke masa ne ya tunzura shi kuma ya sha kai ƙararsa wurin iyayensa.
DSP Lawan ya ce mai shayin ya ɗaure matashin cikin fushi da igiya, ya rinƙa dukansa da sanda har ya ce ga garinku nan.
Ya ce makwabta sun ji kukan Hassan Garba na neman agaji amma sun kasa shiga tsakani har sai da jami’an ‘yan sanda suka ƙariso.
"Da zaran mun kammala bincike za mu gurfanar da mai shayin a gaban kotu domin a hukunta shi daidai da laifinsa," in ji Lawan Shiisu.
Surukar Nuhu Ribadu ta rasu
A wani rahoton Allah ya yiwa, Hajiya Ummu Iya Abubakar, surukar Nuhu Ribadu rasuwa ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2024
Iyalan marigayyar ne suka tabbatar da hakan a wata sanarwa da suka fitar, sun ce za a yi mata janaza a babban masallacin ƙasa da ke Abuja bayan Azahar
Asali: Legit.ng