Gwamnatin Tinubu Ta Gwangwaje ’Yan Najeriya da Tallafin N1.8bn a Jihohi 36

Gwamnatin Tinubu Ta Gwangwaje ’Yan Najeriya da Tallafin N1.8bn a Jihohi 36

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sake ware wani tallafi na mata a jihohin Najeriya 36 da birnin Tarayya Abuja
  • Gwamnatin ta kaddamar da shirin ne karkashin ofishin matar shugaban kasa a Najeriya, Remi Tinubu domin dogara da kai
  • Akalla mata 37,000 ne za su ci gajiyar shirin musamman masu kananan sana'o'i inda kowace za ta samu N50,000 na tallafi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Gwamnatin Tarayya ta ware N1.8bn domin tallafawa mata 37,000 a jihohi 36 da birnin Abuja.

An ware tallafin ne domin taimakawa mata masu kananan sana'o'i inda aka gwangwaje kowace mata da N50,000.

Gwamnatin Tinubu ta ba da tallafin N50,000 ga mata 37,000
Gwamnatin Tinubu ta dake gwangwaje mata 37,000 da tallafi domin dogaro da Kai. Hoto: Rabi'u B Goro.
Asali: Facebook

Halin kunci: Tinubu ya raba tallafi

Kara karanta wannan

Yayin da ambaliya ke rusa gidajen Kaduna, gwamnatin Uba Sani za ta gina sabon birni

Hadimin gwamnan jihar Gombe, Rabi'u B Goro shi ya wallafa bidiyon kaddamar da bikin a shafin Facebook yayin rabon tallafin a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tallafin yana karkashin 'Renewed Hope Initiative' da matar shugaban kasa, Remi Tinubu ke jagoranta domin mata su dogara da kansu.

Matar gwamnan jihar Gombe, Hajiya Asmau Inuwa Yahaya ita ta wakilci Remi Tinubu a taron kaddamar da shirin a birnin Gombe.

Tallafi: Matar gwamna ta shawarci matan Gombe

Asma'u ta shawarci matan da su yi amfani da tallafin domin dogaro da kansu tare da gargadinsu kan yin amfani da kudin wurin biki.

Ta ce za ta tabbatar ta sanya ido domin ganin masu cin gajiyar sun samu tallafin ba tare da matsala ba.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin mai.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Gwamnatoci sun haɗa N100bn domin hana kamfanoni zaluntar mutane

Legit Hausa ta tattauna da wata wacce ta samu tallafi kan irin farin cikin da ta ji.

Maryam Muhammad da ke Gombe ta yi godiya game da samun tallafin domin bunkasa sana'arsu.

"Muna godiya ga matar gwamna da kuma shugaban kasa, tabbas wannan tallafi zai taimaka kuma za mu yi amfani da shi yadda ta dace."

- Maryam Muhammad

Tinubu zai ba gidaje miliyan 3 tallafi

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da raba N50,000 ga iyalan Najeriya har miliyan 3.6.

Tallafin zai zo ne karkashin hukumar tallafawa iyalai domin rage musu radadin halin kunci da ake ciki a fadin kasar

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.