Ambaliya: Ministan Tinubu Ya Fadi Yadda Najeriya Za Ta Shawo Kan Karancin Abinci

Ambaliya: Ministan Tinubu Ya Fadi Yadda Najeriya Za Ta Shawo Kan Karancin Abinci

  • Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya yi nuni da cewa Najeriya za ta samu wadatuwar abinci duk da ambaliyar ruwa
  • Rahoto NEMA ya nuna cewa ambaliyar ruwa ta lalata dubunnan kadada na gonaki yayin da kuma karancin ruwa ya lalata shukoki
  • Kyari ya jaddada cewa gwamnati ta dauki matakai na ganin an mayar da asarar da ambaliyar ruwan ta jawo hanyar noman rani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya jajanta wa dubunnan manoman da ambaliyar ruwa ta lalata musu gonakinsu.

Rahoton baya-bayan nan da NEMA ta fitar ya nuna cewa sama da dubunnan kadada na gonaki suka lalace yayin da mutane 40,000 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa.

Kara karanta wannan

NiMET: Jerin jihohin Arewa 6 da za a tafka ruwa da iska mai karfi, an gargadi mutane

Ministan Tinubu ya yi magana kan hanyar wadatar da abinci a Najeriya
Ministan noma, Abubakar Kyari ya fadi matakan da aka dauka bayan ambaliyar ruwa. Hoto: @SenatorAKyari
Asali: Twitter

Minista ya jajantawa manoma

Abubakar Kyari ya ce iftila'in yana da ban tsoro kuma zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin manoman karkara, inji rahoton NTA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yayin da muke ganin irin barnar da ambaliyar ruwa ta haifar a yankunanmu, tunani na ya koma kan manoman da ruwan ya lalata hanyar gudanar da rayuwarsu.
"Za a ji radadin hakan musamman yadda kowa ke sa rai a noman bana, duk da cewa muna fatan hakan ba zai yi wani tasiri kan wadatuwar abinci na kasar ba."

- A cewar Kyari.

Sanata Abubakar Kyari, ya kuma jajanta wa manoman da suka yi asarar amfanin gonakinsu sakamakon rashin ruwan da aka samu makonnin da suka gabata.

"Mun shiryawa noman rani" - Kyari

Ministan noman ya ce gwamnati za ta kara ba da muhimmanci kan noman rani na 2024/2025 domin mayar da asarar da aka samu sakamakon ambaliyar ruwa a daminar bana.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Ya ce ma’aikatarsa ​​da ta albarkatun ruwa da tsaftar muhalli sun hada kai domin inganta gonakin da ake nomawa a lokacin noman rani.

"Mun rigaya mun kafa wani kwamiti tsakanin ma'aikatun biyu da manyan masu ruwa da tsaki domin wadatar da abinci a kasa ta hanyar noman rani.

- Inji ministan.

Ambaliya ta lalata gidaje 41,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce aƙalla gidaje 41,344 ne ambaliyar ruwa ta lalata a jihohin Arewacin Najeriya.

Jihohin da ambaliyar ta fi shafa a wannan rahoto na hukumar NEMA sun hada da Taraba da Adamawa da ke Arewa maso Gabas, sai Jigawa da ke Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.