Kano: Majalisa ta Nemi Taimakon Gwamna Abba Bayan Iftila'in da Ya Faru a Jihar
- Majalisar dokokin Kano ta nemi gwamnatin jihar ta dauki matakan taimako na gaggawa kan ambaliyar ruwa
- Ɗan majalisa da ke wakiltar Gabasawa, Zakariya Abdullahi ya ce ambaliya ta yi mummunar ta'adi a yankinsa
- Ɗan majalisar ya ce akalla mazabu 3 cikin 11 da ake da su a Gabasawa na cikin mawuyacin hali a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Majalisar dokokin Kano ta miƙa buƙatar gaggawa ga gwamna Abba Kabir Yusuf kan taimakon wadanda ambaliya ta shafa a faɗin jiha.
Ɗan Majalisa mai wakiltar Gabasawa, Zakariyya Abdullahi ne ya mika koken jama'a a zaman Majalisa da ya gudana ranar Litinin, inda ya ce ana wani hali.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa mawuyacin halin da jama'a su ka fada na bukatar tallafin gaggawa daga gwamnatin jiha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Zakariyya Abdullahi ya kara da cewa da yawa daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa na neman mafaka a makarantun firamare a yankin.
Ambaliya ta kassara mazabu a Kano
Majalisar dokokin Kano ta shaidawa gwamna Abba Kabir Yusuf cewa mutane da dama sun rasa gidajensu da gonaki a mazabun da ke sassan jihar.
An gano yadda mamakon ruwan ya shafe gonaki da gidaje a Gabasawa, yayin da wani bawan Allah ya rasa yaransa uku a Panisau, karamar hukumar Ungogo.
Kano: Ɗan majalisa ya nemi dauki
Ɗan Majalisa mai wakiltar Ungogo, Aminu Sa’adu ya nemi ɗaukin Abba Kabir Yusuf wajen taimakawa wadanda ambaliya ya ɗaiɗaita
Haka kuma Hon. Aminu Sa'adu ya nemi gwamnati ta gyara titin da ya tashi daga Bachirawa Tukwane karshen Kwalta zuwa Kududuwafawa a ƙauyen jajira.
Ambaliya ta kashe mutum 49 a Kano
A baya kun ji cewa hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA), ta ce aƙalla mutane 41 ake da tabbacin ambaliya ya kashe su a Arewacin kasar nan.
Haka kuma NEMA ta ce mutane sama da 41,000 sun rasa gidajensu a Jihohin Arewa uku da suka hada da Jigawa da Adamawa da Taraba.
Asali: Legit.ng