Bayan Sarkin Gobir, an Bayyana yadda Yan Bindiga Suka Harbe Ɗan Sarki

Bayan Sarkin Gobir, an Bayyana yadda Yan Bindiga Suka Harbe Ɗan Sarki

  • Rundunar yan sanda a jihar Legas ta fitar da bayani kan yadda yan bindiga suka kashe babban dan wani mai sarauta
  • Yan bindigar sun kashe dan farin sarkin ne mai suna Tijjani Akinloye da tsakar rana kamar yadda rahotanni suka tabbatar
  • Mazauna yankin sun bayyana yadda yan bindigar suka samun nasara a kan Tijjani Akinloye da halin da aka shiga a wajen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Rundunar yan sanda ta yi bayani kan yadda yan bindiga suka kashe dan sarkin Ajiran mai suna Tijjani Akinloye.

Yan sanda sun bayyana cewa an harbe Tijjani Akinloye ne a yankin Chevron yayin da yake tafiya a cikin motarsa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan Sarkin Gobir, 'yan bindiga sun hallaka yaron babban basarake

Yan sanda
An bayyana yadda aka kashe dan sarki a Legas. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mazauna yankin sun shiga zaman dar dar tun da aka harbe Tijjani Akinloye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin yan sanda kan harbe dan sarki

Kakakin yan sanda a jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an kashe Tijjani Akinloye ne da misalin karfe 12:30 na rana.

Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa a daidai lokacin da abin yake faruwa kuma miyagu sun harbe shi ne a lokacin da yake tafiya a motarsa.

Premium Times ta wallafa cewa wasu mutane su hudu dauke da makamai ne suka tare motar Tijjani suka kashe shi har lahira.

Shaidun gani da ido sun yi magana

Wani da ya so a boye sunansa ya bayyana cewa yan bindigar sun bugi motar Tijjani da gangan ne yana fitowa domin duba motar suka bude masa wuta.

Ana cikin haka kuma kowa ya shiga firgici aka wate aka bar Tijjani Akinloye kwance cikin jini kafin ya samu daukin al'umma daga baya.

Kara karanta wannan

Sufetan 'yan sanda ya fusata, ya bayar da zazzafan umarni kan yan Shi'a

Wata ma'aikaciya a yankin ta shawarci mutane da su nisanci wajen domin kaucewa asarar rayuwarsu kuma ta ce ba za ta kara fita aiki ba sai ranar Laraba.

Sarkin Gobir: Za a maka gwamna a ICC

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin matasa a Sokoto sun dauki haramar maka gwamnati a kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta duniya kan kisan Sarkin Gobir.

Jagoran matasan, Sulaiman Shuaibu Shinkafi ya bayyana sharudan da suka ba gwamnatin ta cika a kan lokaci ko kuma su hadu a kotun ICC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng