Rashin Aiki: Gwamnati Ta Shirya Kakkabe Zaman Banza, Matasa Miliyan 2 Za Su Caba
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na samarwa matasan kasar nan ayyukan yi yayin da ake cikin halin kunci
- Gwamnatin za ta samar da ayyukan ne ta ma'aikatar al'adu, fasaha da tattalin arziki domin inganta rayuwar matasa
- Ministar fasaha, al'adu da tattalin arziki, Hannatu Musawa ta ce za a samar da ayyuka sama da miliyan biyu a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta samar da ayyukan yi ga matasan kasar nan fiye da miliyan 2 a ɓangaren nishaɗi da fasaha.
Ministar fasaha, al'adu da tattalin arziki, Hannatu Musawa ce ta bayyana haka, inda ta ce gwamnati na da shirin samarwa matasa abin yi.
A labarin da ya keɓanta ga Daily Trust, Hajiya Hannatu, ta ce za a cimma samar da ayyukan ne ta wadansu hanyoyi guda huɗu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hanyoyin sun haɗa da zuba hannun jari, haɗin gwiwa da bayar da tallafi da kulla alaka da yarjejeniyar yankin kasuwanci ta Afirka (AfCTA).
Yadda za a samar da ayyuka miliyan 2
Gwamnatin Tarayya ta ce shirinta na samawa matasa akalla miliyan 2 ayyukan yi zai bunkasa kasuwanci da karin ayyukan yi a ƙasar nan.
Ministar fasaha, al'adu da tattalin arziki, Hajiya Hannatu Musawa ta ce ɓangaren nishaɗi da fasaha zai ƙara bunƙasa sashen da a yanzu ake samun akalla $3.4bn.
Ministar ta ce yadda za a samar da ayyukan zai kunshi muhimmanci ɓangarorin inganta cigaba, zuba hannun jari da samar da kudin shiga.
Aiki: Ganduje ya ba matasa shawara
A baya kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ba matasa shawara bisa yadda za su ɓullowa matsalar rashin aikin yi da ya addabe su.
Dakta Ganduje ya shawarci matasan da su yi kokarin koyon sana'o'in hannu bayan sun kammala karatunsu domin ba kansu aiki ba sai sun jira a ba su ba.
Ya kara da cewa gwamnati ba za ta iya ba matasan kasar nan ayyukan yi ba, saboda haka su taimaki kansu.
Asali: Legit.ng