Kano: an Barke da Zanga-Zanga da Wakilin Sanusi II Ya Kori Dagatai 3 Babu Dalili
- Mazauna wasu yankuna a karamar hukumar Dawakin Kudu sun nuna damuwa kan matakin sallamar dagatai a kauyukansu da aka yi
- Yan kauyukan Fangido da Daba da Danbagina da kuma Santolo sun bayyana matakin da saba doka da rashin bin ka'ida wurin aiwatarwa
- Hakan ya biyo bayan tube dagatan da wakilin Sarki Sanusi II a Dawakin Tofa, Ado Yusuf Abdullahi ya yi da cewa umarni ne daga sama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Mazauna yankin Fangido da Daba da Danbagina da kuma Santolo a jihar Kano sun ki amincewa da korar dagatai 3 a kauyukansu.
Hakimin da ke kula da kauyukan wanda Sarki Sanusi II ya nada shi ya sallami dagatan da ake ganin ya saba ka'ida da kuma doka.
Wakilin Sanusi II ya sallami dagatai 3
Daily Nigerian ta tattaro cewa Ado Yusuf Abdullahi ya haramta nadin dagatan guda uku daga cikin 30 ba tare da fadin dalili ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku mantaba, bayan sauya dokar masarautun Kano, Dawakin Kudu ta dawo karkashin ikon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Sanusi II ya amince da nadin wakilansa da za su rika kula da dagatai kafin nadin ainihin hakimai a yankunan jihar daban-daban.
Waye ya ba wakilin umarnin tube sarakunan?
Rahotannin sun tabbatar da cewa Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa ya samu umarni ne daga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusu II.
Ya kuma umarci na kusa da wadanda abin ya shafa da su rike ragamar sarautar har zuwa lokacin sake zaben wadanda za su jagoranci masarautun.
Wannan mataki ya jawo rigima tare da fusata mazauna yankunan wadanda suka gudanar da zanga-zanga da yin Allah wadai da matakin.
Wani mazaunin yankin ya ce ana zargin Yusuf Abdullahi da hada baki da shugaban karamar hukumar, Rabiu Dogo wurin daukar matakin.
An fara gayyatar mutane taro Sanusi II
Kun ji cewa a halin yanzu mutane suna ta taya Muhammadu Sanusi II murnar kammala digirinsa na PhD a jami’ar SOAS a Landan.
Bayan ya kammala aikinsa kuma ya gabatar da binciken da ya yi, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya dawo gida jihar Kano.
Asali: Legit.ng