Sufetan 'Yan Sanda Ya Fusata, Ya Bayar da Zazzafan Umarni kan 'Yan Shi’a

Sufetan 'Yan Sanda Ya Fusata, Ya Bayar da Zazzafan Umarni kan 'Yan Shi’a

  • Shugaban yan sanda, Kayode Egbetokun ya ba jami'ansa zazzafan umarni kan yan kungiyar Shi'a bayan sun yi arangama a Abuja
  • Rundunar yan sanda ta zargi yan kungiyar Shi'a da kai musu farmaki a yayin da suka fito tattaki a ranar Lahadi a birnin tarayya
  • Haka zalika rundunar yan sanda ta yi zargin 'yan kungiyar Shi'a sun kona mata motoci yayin da suka yi arangamar a yankin Wuse

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar yan sanda ta fitar da sanarwa kan yan Shi'a bayan sun yi arangama a birnin tarayya Abuja.

Sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya ce kisan yan sanda ba abu ne da hukuma za ta lamunta a fadin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tunkari Abuja da tsakar rana, sun fafata da yan sanda

Yan sanda
IGP Kayode ya yi umarnin kamo wandanda suka kashe yan sanda. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro abin da IGP Kayode Egbetokun ya fada ne a cikin wani sako da rundunar yan sanda ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IGP Kayode ya yi umarni kan yan Shi'a

IGP Kayode Egbetokun ya ba yan sanda umarnin tabbatar da cafkewa tare da hukunta yan Shi'an da ake zargi da kashe yan sanda biyu.

Sufeton yan sandan ya ce sun tsokano tsuliyar dodo tun da suka kashe yan sanda kuma za a tabbatar sun dandana kuɗarsu.

An kama mutane 97 kan rikicin yan Shi'a

Daily Trust ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta bayyana cewa biyo bayan rikicinsu da yan Shi'a ta kama mutane 97 da ake zargi da hannu a lamarin.

Haka zalika rundunar ta bayyana cewa ta kama makamai da dama ciki har da arduna da wuƙaƙe da aka yi amfani da su wajen kai hari wa yan sandan.

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

Sakon Kayode ga iyalan yan sanda

IGP Kayode Egbetokun ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan yan sandan da suka rasu yayin arangamar da kuma addu'a ga wandada suka ji rauni.

Sai dai wasu yan kungiyar Shi'a sun nuna cewa ba su da hannu a wajen kisan yan sandar a yayin da suke tattaki a Abuja a ranar Lahadi.

An yi rikici a kasuwar Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rikici ya kara barkewa a kasuwar Wuse da ke birnin tarayya Abuja kan shugabanci da ake ƙoƙarin nada mutane.

Rundunar yan sanda ta isa kasuwar domin kwantar da tarzomar amma duk da haka an ruwaito cewa mutane sun kulle shagunansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng