Rikicin Abuja: Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da wasu 'yan Shi'a bisa tayar da zaune tsaye

Rikicin Abuja: Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da wasu 'yan Shi'a bisa tayar da zaune tsaye

- Rundunar yan sanda ta gurfanar da wasu mambobin mabiya akidar Shi'a (IMN) a gaban kotu, bisa zarginsu da tayar da zaune tsaye

- Daga cikin wadanda ake karar, akwai mata masu dauke da juna biyu da kuma masu shayarwa, sai dai sun ce sam basu aikata wannan laifi ba

- Kotu ta bayar da belinsu akan N50,000, wasu kuma akan N500,000

Rundunar yan sanda ta babban birnin tarayya Abuja, ta gurfanar da wasu mambobin mabiya akidar Shi'a (IMN) a gaban kotu, bisa zarginsu da tayar da zaune tsaye a cikin jama'ar da ke zaune a babban birnin.

A cewar takarar karar da aka gabatar gaban kotun majistire da ke Zone 2, Wuse, a ranar Alhamis, wadanda ake zargin su 130, ana zarginsu da yiwa jami'an tsaro ruwan duwatsu biyo bayan umurnin da aka basu na tarwatsewa daga zanga zangar da suka gudanar daga ranar Asabar zuwa Laraba.

KARANTA WANNAN: Aisha Buhari: Sai da gwamnatin Buhari ta zo 'yan Nigeria suke shan romon demokaradiyya

Daga cikin wadanda ake karar, akwai mata masu dauke da juna biyu da kuma masu shayarwa, sai dai sun ce sam basu aikata wannan laifi da ake zarginsu da aikatawa ba.

Wadanda ake zargin, da aka gurfanar da su a dakunan shari'a daban daban da ke cikin kotun, an bayar da belinsu akan N50,000, wasu kuma akan N500,000.

Cikakken labarin yana zuwa...

Yan shi'a na gudanar da zanga zanga a Abuja
Yan shi'a na gudanar da zanga zanga a Abuja
Asali: Facebook

Sai dai, idan ba a manta ba, Legit.ng Hausa, ta ruwaito maku cewa ‘yan Kungiyar Ismlamic Movement of Nigeria (IMN) da aka fi sani da 'yan Shi'a, sun bayyana cewa ba za su taba daina tattakin da su ke gudanarwa a babban birnin tarayya Abuja ba har sai gwamnati ta sako shugabansu Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa daga inda ake tsare su tun a shekarar 2015.

Bayan artabun da su kayi da jami’an tsaro, daya daga cikin shugabanin kungiyar, Abdullahi Muhammad ya shaidawa manema labarai cewa ba za su dena tattakin ba duk da harin da jami’an tsaro ke kai musu.

A yayin wannan zanga zanga tasu, an samu salwantar rayuka akalla 50.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa Wannan sauyi ne da zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Kasance tare da shafinmu na Legit.ng Hausa don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng