Majalisa Ta Gaji da Halin 'Yan Kwangila, Ana Shirin Daukar Mataki kan Masu Algus

Majalisa Ta Gaji da Halin 'Yan Kwangila, Ana Shirin Daukar Mataki kan Masu Algus

  • Majalisar wakilai ta yi tir da irin aikin da 'yan kwangila su ka yi a hedkwatar gidan gyaran hali da ke Abakaliki
  • Shugaban kwamitin sanya idanu kan gidajen gyaran hali da tarbiyya na majalisa, Chinedu Oga ya ce ba su ji dadi ba
  • 'Dan majalisar ya bayyana haka ne bayan ganin aikin da wani dan kwangila ya yi a jihar Ebonyi, ya nemi a gyara aikin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ebonyi - Kwamitin majalisar wakilai da ke sanya ido kan harkokin gidajen gyaran hali da tarbiyya ya ce ba zai lamunci ha'inci ba.

Shugaban kwamitin, Chinedu Oga ne ya bayyana rashin jin dadin bayan duba aikin a hedkwatar hukumar kula da gidan gyaran hali da ke Abaliki.

Kara karanta wannan

Digiri dan Kwatano: Gwamnati ta lissafa jami'o'in Benin, Togo da ta amince da su

Majalisa
Majalisa ta gargadi yan kwangila masu aiki da ha'inci Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Hon. Oga wanda ke wakiltar Ikwo/Ezza ta kudu ya ce 'ya'yan kwamitin sun kai ziyarar aiki domin duba ayyuka a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma sun duba yadda za a inganta gidajen gyaran hali da rayuwar daurarrun da ke cikinsu.

Majalisa ta dauki mataki kan yan kwangila

Majalisar wakilai ta dauki mataki kan yan kwangilar da su ka yi aiki da algus a Abaliki da ke jihar Ebonyi, inda ya ce ba su ji dadin abin da su ka gani ba.

Shugaban kwamitin kula da gidajen gyaran hali na kasar nan a majalisar, Hon. Chinedu Oga ya ce an dawo da yan kwangilar domin gyara aikin daidai da tsari.

Hon. Oga ya ce duk dan kwangilar da ba ya aikinsa yadda ya dace, zai tilasta masu shaidawa gwamnati cewa ta sanya shi cikin kundin marasa aiki da inganci.

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Majalisa ta tona masu boye tallafi

A baya mun ruwaito cewa majalisar dattawan kasar nan ta bayyana cewa wasu tsirarun mutane ne handame tallafin abincin da shugaban kasa ke fitarwa.

Mataimakin shugaban majalisa, Barau Jibrin ne ya bayyana haka, inda ya ce yanzu haka akwai sabon tallafin abinci da za a rabawa mazauna kananan hukumomin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.