Miyagu Za Su ga Ta Kansu, Rundunar Yan Sanda Ta Daukarwa Yan Najeriya Alwashi

Miyagu Za Su ga Ta Kansu, Rundunar Yan Sanda Ta Daukarwa Yan Najeriya Alwashi

  • Rundunar yan sandan kasar nan ta jaddada kudirinta na dawo da zaman lafiya yankunan da ke fama da ta'addanci
  • Babban Sufeton yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka, inda ya dauki alkawarin aiki tukuru
  • Alkawarin rundunar yan sandan na zuwa a lokacin da rashin tsaro ke kara samun gurbi a jihohin Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Rundunar yan sandan kasar nan ta sha alwashin tabbatar da an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka, inda ya ce za su rubanya kokarinsu har sai an tabbatar da tsaron yan kasar nan.

Kara karanta wannan

Sufetan 'yan sanda ya fusata, ya bayar da zazzafan umarni kan yan Shi'a

Police
Rundunar yan sanda ta dauki alkawarin kakkabe rashin tsaro daga kasar nan Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa babban Sufeton ya dauki alkawarin ne a lokacin da ya ke mika daliban jami'ar Maiduguri da na Jos da aka sace a Binuwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shaidawa manema labarai cewa za su sake shirin tunkarar rashin tsaro kai tsaye, har sai an ga bayan miyagu a sassan kasar.

"Za mu cigaba da yakar miyagu," Yan sanda

Rundunar yan sandan kasar nan ta ce za ta cigaba da yakar yan ta'adda har sai an yi nasarar magance rashin tsaron da ya addabi kasar nan, The Nation ta wallafa.

Babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka, inda ya ce ba za su zuba ido yan ta'adda su na cin karensu babu babbaka ba.

Babban Sufeton ya bukaci yan Najeriya su zama masu sa ido, sannan su taimakawa jami'an tsaro wajen kare dukiya da rayukansu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun nuna bajintarsu, an gano yadda aka kashe fitinannen dan ta'adda

Yan sanda sun kwato mutane 22 daga miyagu

A baya kun ji cewa rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana nasarar da ta samu wajen kwato mutane 22 da yan bindiga su ka yi garkuwa da su.

Wannan na zuwa ne a yunkurin jami'an tsaro na ceto likitoci dalibai 20 da aka sace a Binuwai, inda aka samu ceto karin mutum biyu da ke hannun miyagun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.