Yan Sanda Sun Nuna Bajintarsu, An Gano Yadda Aka Kashe Fitinannen Dan Ta'adda

Yan Sanda Sun Nuna Bajintarsu, An Gano Yadda Aka Kashe Fitinannen Dan Ta'adda

  • Rundunar 'yan sandan kasar nan ta yabi kanta wajen ceto likitoci dalibai da yan bindiga su ka sace a jihar Binuwai a hanyarsu ta zuwa Enugu
  • Shugaban 'yan sandan kasar nan, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa sun yi nasarar sheke fitinannen dan ta'adda tare da damke wasu miyagu
  • Babban Sufeton ya kara da cewa wadanda aka kama su na hannu, saboda haka za a zurfafa bincike domin samun nasarar shako wasu daga cikin miyagun

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Babban Sufeton kasar nan, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa sun yi nasarar kashe kasungurmin dan ta'adda a lokacin da jami'ansu su ka kai dauki ga daliban da aka sace.

Kara karanta wannan

Miyagu za su ga ta kansu, Rundunar yan sanda ta daukarwa yan Najeriya alwashi

'Yan bindiga sun tare likitoci dalibai guda 20 a jihar Binuwai a hanyarsu ta zuwa Enugu, sannan su ka yi awon gaba da su.

Police
Yan sanda sun sheke fitinannen dan ta'adda Hoto: Nigeria Police
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a bayaninsa bayan ceto daliban, babban Sufeto Egbetokun ya shaidawa shugabannin jami'o a Abuja, ya ce sun ba 'yan ta'addan kashi yayin ceton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara cewa an cafke wasu miyagu guda biyu, wanda yanzu haka aka taho da su hedikwatar rundunar domin zurfafa bincike.

Yadda yan sanda su ka ceto dalibai

Rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana ceto mutane 22 daga hannun masu garkuwa da mutane ba tare da biyan ko sisi a matsayin kudin fansa ba.

Nigeria Tribune ta wallafa cewa babban Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka, inda ya ce masu garkuwa da mutane da aka kama za su taimaka wajen bincike.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

Ya kara da cewa sun samu wasu mutane biyu a hannun yan bindigar, wanda aka ceto su tare da dalibai likitoci guda 20 da ake je cetowa.

Yan sanda sun kashe miyagu

A baya mun ruwaito cewa rundunar yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar sheke miyagu biyu yayin dakile yunkurinsu na sace wasu mutane biyar a karamar hukumar Malumfashi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa jami'ansu sun amsa kiran kai dauki kauyen Layin Minista bayan yan ta'addan sun kai masu hari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.