'Yan Sanda Sun Yi Artabu da Miyagu, An Sheke 'Yan Bindiga a Katsina
- Rundunar yan sandan Katsina ta yi nasarar dakile sace mutane biyar a jihar bayan ta amsa kiran kan dauki
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Abubakar Sadiq ne ya bayyana haka ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin
- Kakakin ya kara da cewa mazauna kauyen Layin Mininsta a karamar hukumar Malumfashi ne su ka nemi agajinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Yan sanda a jihar Katsina sun dakile harin yan ta’adda har guda biyu, tare da ceto wadanda aka yi yunkurin sacewa a Katsina.
Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq ne ya bayyana haka ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.
Jaridar Punch ta wallafa cewa ASP Sadiq ya ce sun samu kiran gaggawa ne daga mazauna Layin Minista a karamar hukumar Malumfashi, inda aka yi yunkurin sace mutane guda biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’in hulda da jama’a na yan sandan ya ce ba su bata lokaci ba wajen kai agajin gaggawa, inda su ka fatattaki yan ta'addan.
Katsina: Yan sanda sun ceto mutum 5
Rundunar 'yan sandan Katsina ta bayyana cewa jami'anta sun ceto wasu mutane biyar da masu garkuwa da mutane su ka yi yunkurin sacewa a jihar.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Sadiq Abubakar ne ya bayyana haka, inda ya ce miyagun sun budewa jami'ansu wuta a lokacin da su ka kai agaji.
ASP Abubakar ya ce amma jami'ansu sun mayar da harbin, inda aka yi nasarar korar 'yan bindigar, tare da tsintar gawarwakin biyu daga cikinsu.
Yan Sanda sun ceto mutum 30 a Katsina
A baya kun ji cewa rundunar yan sandan Katsina ta fusata da yadda yan bindiga ke kai hare-hare babu kakkautawa sassan jihar, inda aka yi kokarin dakile mugun aikin da su ke yi.
A hare-haren da yan sandan su ka yi kokarin dakilewa, sun yi nasarar ceto mutum 30 da 'yan ta'addan su ka yi garkuwa da su a kananan hukumomi guda biyu da ke jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng