Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Miyagun 'Yan Ta'adda a Jihar Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Miyagun 'Yan Ta'adda a Jihar Kaduna

  • Dakarun sojoji da ke yaƙi da ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya a Kaduna sun samu gagarumar nasara kan miyagun
  • Sojojin a yayin wani samame da suka kai a jihar, sun yi nasarar hallaka wani ɗan ta'adda mutum ɗaya har barzahu
  • Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa a hannun ƴan ta'addan tare da raunata da dama daga cikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojojin Najeriya na runduna ta ɗaya a jihar Kaduna sun samu nasarar hallaka wani ɗan ta'adda.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa a wani samame da suka kai a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun hallaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a Arewacin Najeriya

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna
Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda sojoji suka ragargaji ƴan ta'adda

Muƙaddashin kakakin rundunar, Laftanal Kanal Musa Yahaya ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Kaduna, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ya bayyana cewa an kai samamen ne a yankin Sabon Birni, Dogon Dawa, Maidaro, Ngede Alpha da Rafin Kaji a ranar Lahadi, 25 ga watan Agustan 2024, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya bayyana cewa a yayin samamen dakarun sojoji sun yi arangama da ƴan ta'adda inda suka hallaka ɗaya daga cikinsu, yayin da sauran suka arce ɗauke da raunuka.

Sojoji sun ƙwato makamai

Laftanal Kanal Musa Yahaya ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun ƙwato bindigu ƙirar AK47 guda huɗu, bindigar PKT mai alburusai 86, babura guda biyu.

Sauran abubuwan da aka ƙwato daga hannun ƴan ta'addan sun haɗa da wayar hannu ƙirar Techno guda ɗaya, rediyo guda ɗaya da katin waya na N5,000 na layin Airtel.

Kara karanta wannan

Kisan Sarkin Gobir: 'Yan sanda sun cafke masu zanga zanga, sun fadi dalili

Sojoji sun hallaka kwamandojin ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun hallaka manyan kwamandojin ƴan ta'adda biyar a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sojojin sun hallaka kwamandojin ne tare wasu ƴan ta'adda 35 a wasu hare-haren da jiragen yaƙin rundunar suka kai a yankin Arina, da ke Kudancin Tumbun na jihar Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng